An kai hari kan ayarin motocin fitaccen ɗan siyasar adawa a Nijeriya, Peter Obi, a jihar Cross River da ke kudancin ƙasar, inda rundunar ’yan sanda ta kama wani mutum da ake zargi da hannu a lamarin.
Lamarin ya faru ne ranar Laraba, jim kaɗan bayan Obi da tawagarsa sun kai ziyara fadar Obong na Calabar, a lokacin da suke kan hanyarsu ta zuwa wani taro da jam’iyyarsa ta Nigeria Democratic Congress (NDC) ta shirya.
Rahotannin kafafen yaɗa labarai sun bayyana cewa wasu mahara ɗauke da adduna da sanduna sun far wa ayarin motocin da duwatsu da wasu abubuwa, lamarin da ya haddasa farfashewar gilashin wasu motocin tare da firgita magoya bayan Obi da ’yan kasuwa a yankin.
Rundunar ’yan sandan jihar Cross River ta ce ta kama wani mutum mai shekaru 27 mai suna Victor Edet Yellow Duke, bisa zargin hannu a harin.
Rundunar ta ƙara da cewa ana ci gaba da gudanar da bincike domin gano ƙarin bayanai da kuma tabbatar da duk waɗanda ke da hannu a lamarin.
’Yan siyasa na fuskantar hare-hare gabanin zaɓen 2027
Wannan hari ya zo ne kwanaki kaɗan bayan makamancin haka da aka kai wa Omoyele Sowore, ɗan takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam’iyyar African Action Congress (AAC), a jihar Ekiti.
Jam’iyyun siyasa a Nijeriya na ci gaba da shirye-shiryen tunkarar babban zaɓen shekarar 2027, inda Shugaba Bola Tinubu ke neman wa’adi na biyu a ƙarƙashin jam’iyyar APC mai mulki.
Wasu fitattun ’yan siyasar adawa, ciki har da tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar da Peter Obi, sun bayyana manufofinsu kan yadda za a magance matsalolin tsaro, matsin tattalin arziki da ƙalubalen shugabanci a ƙasar.
Ana sa ran matsalolin tsaro da farfaɗo da tattalin arziki za su kasance cikin muhimman batutuwan da za su mamaye muhawarar siyasa yayin da ƙasar ke shirin gudanar da babban zaɓen 2027.
