A wata tattaunawa ta musamman da sashen Pidgin na BBC, tsohon ministan sufuri kuma tsohon gwamnan jihar Ribas ya yi iƙirarin cewa manufar shirin ita ce haifar da ruɗani da kuma hana jam’iyyarsu samun damar fafatawa a zaɓen.
BBC ta nemi jin ta bakin EFCC kan zargin, amma har zuwa lokacin wallafa wannan rahoto, hukumar ba ta mayar da martani ba.
Da aka tambaye shi ko yana fargabar yiwuwar kama shi, Amaechi ya ce ba ya jin tsoro ko shakka game da hakan.
Ya ce: "Su zo mana, ina nan ina jiransu. Ai ba wai za su ɗauke ni su tafi da ni ba ne? Manufarsu kawai ita ce su tabbatar ba mu kayar da su ba."
Kalaman Amaechi na zuwa ne a daidai lokacin da jam’iyyar ADC ke fuskantar ƙalubalen shari’a da ka iya shafar damar shiga zaɓen shekarar 2027.
A ranar 5 ga Nuwamban 2026, Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta soke shugabancin jam’iyyar ADC ƙarƙashin jagorancin David Mark, tare da rushe matakan da kwamitin riƙon ƙwarya na ɓangarensa ya ɗauka.
Wannan mataki ya haɗa da batutuwan da suka shafi zaɓen fidda gwani na shugaban ƙasa, wanda ya samar da Atiku Abubakar a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC a zaɓen 2027, tare da zaɓar Rotimi Amaechi a matsayin abokin takararsa.
