Akpabio ya bayyana hakan ne yayin zaman Majalisar Dattawa ranar Talata, bayan Sanatan da ke wakiltar Jigawa ta Arewa maso Yamma, Babangida Hussaini, ya yi zargin cewa an ga wani ɗan takarar jam'iyyar African Democratic Congress (ADC) a jihar yana ɗauke da bindiga a wajen gangamin neman zaɓe.
Shugaban Majalisar Dattawan ya ce INEC na da ikon hana ɗan takara shiga zaɓe idan ta samu sahihan hujjoji da ke nuna cewa shi ko wakilansa sun haddasa tashin hankali ko kuma sun tunzura mutane.
Ya kuma buƙaci a gudanar da bincike kan hoton da ake zargin ya nuna ɗan takarar yana riƙe da bindiga, domin tabbatar da sahihancinsa, musamman ganin yiwuwar an ƙirƙire shi ta amfani da fasahar basirar ɗan'adam (AI).
Akpabio ya jaddada cewa ya kamata a aiwatar da tanade-tanaden Dokar Zaɓe ta 2026 yadda ya kamata, ba tare da nuna bambanci tsakanin jam'iyyun siyasa ba.
Wannan na zuwa ne yayin da Majalisar Dattawa ke nuna damuwa kan ƙaruwar rikicin siyasa da hare-hare kan wasu manyan ƴan siyasa gabanin zaɓen shekarar 2027.
Majalisar ta kuma buƙaci jami'an tsaro su gudanar da bincike kan hare-haren da aka ruwaito an kai wa Shugaba Bola Tinubu, tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar da Peter Obi, domin gano waɗanda suka aikata su da kuma waɗanda ake zargin sun ɗauki nauyin rikice-rikicen.
