Tsagin David Mark ya shigar da ƙorafi mai buƙatu 17 a gaban kotun, inda yake ƙalubalantar hukuncin da Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yanke ranar 5 ga Nuwamba, 2026, wanda ya bayyana a matsayin kuskure.

A hukuncin, Babbar Kotun Tarayya ta soke shugabancin tsagin David Mark da kuma matakan da ya ɗauka, ciki har da tsayar da Atiku Abubakar a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa.

Sai dai a ƙarar da ya shigar gaban Kotun Ɗaukaka Ƙara, tsagin ADC na David Mark ya ce Babbar Kotun Tarayya ba ta da hurumin sauraron takaddamar shugabancin jam’iyyar.

A wata sanarwa da Daraktan Sadarwa na kwamitin yaƙin neman zaɓen Atiku, Phrank Shaibu, ya fitar ranar Talata, jam’iyyar ta ce tana kuma ƙalubalantar hukuncin da ya bai wa Bala Gombe damar gyara ƙarar da ya shigar tun farko, duk da cewa har yanzu akwai ƙalubale kan hurumin kotun na sauraron shari’ar.

ADC ta yi gargaɗin cewa idan aka bai wa INEC damar aiwatar da hukuncin ranar 5 ga Nuwamba kafin Kotun Ɗaukaka Ƙara ta yanke hukunci kan batutuwan da aka gabatar, hakan na iya rage tasirin ƙarar da ta ɗaukaka tare da jefa ’yan takararta cikin rashin tabbas.

Saboda haka, jam’iyyar ta buƙaci Kotun Ɗaukaka Ƙara ta tabbatar da cewa bayanan shugabancinta da na ’yan takararta sun ci gaba da kasancewa yadda suke a halin yanzu har sai an kammala shari’ar.