AMMASCO RADIO NEWSROOM

top stories

Peter Obi Ya Bukaci Tinubu Ya Haƙura Da Takarar 2027

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar NDC , Peter Obi, ya buƙaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya haƙura da neman wa'adi na biyu a zaɓen shekarar 2027 , yana mai cewa shugaban ya gaji kuma ba shi da ƙarfin da zai iya magance matsalolin tattalin arziki da rashin tsaro da ƙasar ke fuskanta. A wata hira da gidan talabijin na Channels Television , Obi ya ce Tinubu na yanzu ba irin shugaban da ya yi mulkin Jihar Legas ba ne, yana mai zargin gwamnatinsa da gaza shawo kan matsalolin talauci, yunwa da rashin tsaro. Obi ya ce rahotannin ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa sun nuna cewa miliyoyin 'yan Najeriya na f

Ghana Ta Fara Kwashe 'Yan Kasarta 1,000 Daga Afirka Ta Kudu.

Gwamnatin Ghana ta sanar da cewa karin 'yan ƙasarta 1,000 da ke aiki a matsayin baƙin haure a Afirka ta Kudu za su fara komawa gida a ranakun Lahadi da Litinin , sakamakon ci gaba da zanga-zangar da ta rikide zuwa tashin hankali kan baƙin haure. Tun da farko, hukumomin Ghana sun yi nasarar kwashe 'yan ƙasa 926 daga Afirka ta Kudu, yayin da gwamnatin ta yi Allah wadai da hare-haren da suka yi sanadin asarar rayuka a ƙasar. A cikin wata sanarwa da Ma'aikatar Harkokin Wajen Ghana ta fitar a daren Asabar, ta bayyana cewa jirage na musamman za su fara isa Ghana a ranakun Lahadi da Litinin domin daw

Gwamnatin Jihar Sokoto Ta Nesanta Kanta Daga Ayyukan Wani Mai Sihiri Da Aka Fi Sani Da "Mai Shaho"

Gwamnatin Jihar Sokoto ta bayyana cewa ba ta da wata alaƙa da wani mai sihiri da aka fi sani da suna Mai Shaho , bayan wani faifan bidiyo da ya bazu a kafafen sada zumunta. A cikin bidiyon, an ga mutumin yana binne bunsuru da rai tare da ikirarin cewa ɗan takarar gwamna na jam'iyyar ADC a jihar ba zai yi nasara ba. A cikin wata sanarwa da Daraktan Hulɗa da Jama'a na Gidan Gwamnatin Sokoto, Abubakar Bawa , ya fitar, gwamnatin ta nesanta kanta da mutumin da kuma duk wani abu da ya shafi ayyukansa. Sanarwar ta jaddada cewa gwamnatin jihar ba ta goyon bayan sihiri ko duk wani aiki da ya saɓa wa ko

Amurka Da Iran Sun Na Tattaunawar Sulhu Bayan Shawarar Pakistan Da Qatar

Amurka da Iran sun mayar da martani mai kyau ga wata shawarar sasanci da ƙasashen Pakistan da Qatar suka gabatar domin kawo ƙarshen rikicin da ke tsakaninsu, inda rahotanni suka nuna cewa ɓangarorin biyu sun amince da amfani da tattaunawa da diflomasiyya wajen rage zaman ɗar-ɗar. Kamfanin dillancin labarai na Anadolu ya ruwaito cewa shirin sasancin ya haɗa da komawa yanayin da ake ciki kafin ɓarkewar sabon rikicin da ya ɗauki kwanaki 17 , tare da komawa teburin tattaunawa domin nemo mafita ta lumana. Majiyoyi sun bayyana cewa an dakatar da hare-haren da Amurka da Iran ke kai wa juna na tsawon

Operation FANSAN YAMMA Sun Ceto Mutane 48 Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Zamfara

Dakarun Joint Task Force North West – Operation FANSAN YAMMA sun ceto mutane 48 da aka yi garkuwa da su bayan gaggawar kai ɗauki sakamakon harin da 'yan ta'adda suka kai ƙauyen Magami da ke Ƙaramar Hukumar Kaura Namoda a Jihar Zamfara, a safiyar ranar 26 ga Yuli, 2026 . A cewar wata sanarwa da Rundunar ta fitar, dakarun Sector 2 sun tashi kai tsaye bayan samun kiran gaggawa cewa wasu 'yan ta'adda da ke kan babura kusan 40 sun mamaye ƙauyen tare da tattara mazauna domin yin garkuwa da su zuwa cikin daji. Da isar dakarun wurin, nan take suka fafata da maharan a wani mummunan artabu, lamarin da y

Operation HADIN KAI: Wani Babban Jami'in Kuɗi Na ISWAP Ya Miƙa Wuya Ga Sojoji

Dakarun Operation HADIN KAI sun samu wata babbar nasara bayan wani babban jami'in kula da harkokin kuɗi na ƙungiyar ISWAP ya miƙa wuya ga sojoji, lamarin da ke nuna ci gaba da raunana ƙarfin ƙungiyar sakamakon hare-haren da dakarun ke ci gaba da kai wa. A cewar wata sanarwa da Hedikwatar Operation HADIN KAI ta fitar, mutumin ya miƙa wuya ga dakarun Bataliya ta 3 ƙarƙashin Rundunar 24 Task Force Brigade da misalin ƙarfe 6:45 na safiyar ranar 25 ga Yuli, 2026 , a kan hanyar Ladari–Jegarawa–Tunokalia da ke babban titin Gamboru–Wulgo . Bayanan farko sun nuna cewa mutumin shi ne babban jami'in kula

Gwamnatin Tarayya Ta Ƙaddamar Da Kwamitin Tsara Dokar Gyaran VAT Ta 2026

Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da wani Kwamitin Haɗin Gwiwar Ma'aikatu domin tsara Dokar Gyaran Harajin Ƙarin Daraja (VAT Modification Order) ta shekarar 2026 , a wani muhimmin mataki na aiwatar da sabbin dokokin haraji na Najeriya. Ministan Kuɗi kuma Ministan Kula da Tattalin Arziki, Taiwo Oyedele , ne ya rantsar da mambobin kwamitin, wanda aka ɗora wa alhakin nazarin tanade-tanaden da suka shafi kayayyaki da ayyukan da aka keɓe daga biyan VAT ko aka sanya musu harajin sifili (Zero-rated) ƙarƙashin Dokar Haraji ta Najeriya. Ana kuma sa ran kwamitin zai gabatar da shawarwari kan yadda za a sama

INEC Ta Sanar Da Gwajin Tantance Masu Zaɓe Kafin Zaɓen Gwamnan Jihar Osun

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta sanar da cewa za ta gudanar da gwajin tantance masu zaɓe (Mock Accreditation Exercise) kafin zaɓen gwamnan Jihar Osun da za a yi ranar 15 ga Agusta, 2026 , domin tantance matakin shirinta. A cikin wata sanarwa da Shugaban Sashen Ilimantar da Masu Zaɓe, Yaɗa Labarai, Jinsi da Haɗa Kowa, Ariyo Rufus , ya sanya wa hannu, INEC ta ce za a gudanar da gwajin ne ranar Asabar, 1 ga Agusta, 2026 , a wasu rumfunan zaɓe da aka zaɓa a ƙananan hukumomi 12 da ke faɗin gundumomin sanata uku na jihar. Ƙananan hukumomin da za a gudanar da gwajin sun haɗa da Osogbo,

Ma'aikatar Tsaro Ya Jaddada Aniyarta Na Bunƙasa Jami'ar Sojojin Najeriya Da Ke Biu

Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa (mai ritaya) , ya sake jaddada ƙudirin Gwamnatin Tarayya na mayar da Jami'ar Sojojin Najeriya da ke Biu (NAUB) ta zama cibiyar koyarwa ta ƙwarai wajen horar da jami'an soja da fararen hula. Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Mai Bai wa Ministan Tsaro Shawara kan Harkokin Yaɗa Labarai, Leah Katung-Babatunde , ta fitar. A cewar sanarwar, Janar Musa ya bayyana hakan ne yayin da ya karɓi baƙuncin mambobin Majalisar Gudanarwar jami'ar a hedikwatar Ma'aikatar Tsaro da ke Abuja. Ya tabbatar musu da ci gaba da ba jami'ar cikakken goyon baya, yana mai cewa N

Harry Kane Na Dab Da Tsawaita Zamansa A Bayern Munich

Gwarzon ɗan wasan gaba kuma kyaftin ɗin Ingila, Harry Kane , na ci gaba da tattaunawa da Bayern Munich kan sabunta kwantaraginsa, yayin da zakarun Bundesliga ke son ya ci gaba da zama a ƙungiyar. Kwantaragin Kane na yanzu zai ƙare ne a ƙarshen kakar wasa mai zuwa, sai dai rahotanni na nuna cewa bangarorin biyu na da kyakkyawar fahimta, kuma ana sa ran za a kammala yarjejeniyar cikin makonni masu zuwa. Kane ya koma Bayern Munich daga Tottenham Hotspur a shekarar 2023 kan kuɗi kusan fam miliyan 86 , kuma tun daga lokacin ya taka muhimmiyar rawa wajen nasarorin da ƙungiyar ta samu. Ya taimaka wa

Kotun CAS Ta Sanya Ranar Sauraren Ƙarar Senegal Kan Kofin AFCON 2025

Kotun Sauraren Kararrakin Wasanni ta Duniya (CAS) ta sanya 8 ga watan Oktoba a matsayin ranar da za ta fara sauraren ƙarar da Senegal ta ɗaukaka kan hukuncin da ya ƙwace mata kofin gasar AFCON 2025 . Tun farko, Senegal ce ta doke Morocco da ci 1-0 a wasan ƙarshe na gasar da aka kammala a watan Janairu. Sai dai daga bisani Hukumar Kwallon Kafa ta Afirka (CAF) ta sauya hukuncin, tare da ayyana Morocco a matsayin zakara bayan ta bai wa Senegal hukuncin shan kashi da ci 3-0 . Lamarin ya samo asali ne bayan 'yan wasan Senegal sun fice daga filin wasa sakamakon rashin amincewa da fenaritin da aka ba

Trump Ya Dakatar Da Ƙara Faɗaɗa Hare-Haren Sojin Amurka Kan Iran

Rahotanni da dama daga Amurka sun bayyana cewa Shugaban ƙasar, Donald Trump, ya yanke shawarar dakatar da ƙara faɗaɗa hare-haren sojin Amurka kan Iran, aƙalla a halin yanzu. A cewar rahotannin, Trump ya ɗauki wannan mataki ne a ranar Juma'a bayan wasu manyan jami'an gwamnati sun nuna damuwa kan raguwar makamai masu linzami na kariya na Patriot , waɗanda ke da tsadar gaske, tare da fargabar cewa ci gaba da hare-haren na iya janyo rashin jituwa tsakanin Amurka da ƙawayenta na ƙasashen Larabawa da ke yankin Tekun Fasha. Sai dai har zuwa yanzu, babu wata sanarwa a hukumance da Fadar White House ta

Sufeto Janar Ya Umarci Ƴan Sanda Su Murƙushe Masu Rike Makamai Ba Bisa Ƙa’ida Ba

Sufeto Janar na Ƴan Sandan Najeriya, Olatunji Disu , ya umarci dukkan jami’an ‘yan sanda a faɗin ƙasar nan da su ɗauki mataki mai tsauri kan duk wanda aka samu yana riƙe da makamai ba bisa ƙa’ida ba, domin daƙile ayyukan ta’addanci da sauran laifukan da ke barazana ga tsaron al’umma. Ya ce jami’an su yi aiki da tanadin Force Order 327 wajen gudanar da ayyukansu, musamman domin murƙushe masu aikata laifuka da kuma tabbatar da zaman lafiya, musamman a Jihar Benue da ke fama da hare-hare. Sufeto Janar ɗin ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da ya yi da Gwamnan Jihar Benue, Hyacinth Alia , a bir

Kotu Ta Dakatar da Yunkurin Tsige Shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa

Wata Babbar Kotu a lardin Western Cape na Afirka ta Kudu ta dakatar da shirin Majalisar Dokokin ƙasar na tsige Shugaba Cyril Ramaphosa , kan zarge-zargen rashin ɗa'a da ake yi masa. A hukuncin wucin gadi da kotun ta yanke ranar Juma'a, ta umarci majalisar da ta dakatar da duk wani mataki na tsige shugaban har sai an kammala sauraron ƙarar da Ramaphosa ya shigar yana ƙalubalantar rahoton kwamitin bincike. Rahoton kwamitin ya bayyana cewa akwai hujjojin da ke nuna shugaban na da tambayoyin da zai amsa dangane da satar kuɗaɗe da aka yi daga gonarsa ta Phala Phala a shekarar 2020. Lamarin ya shafi

Har Yanzu Ana Jiran Ceto Ɗaliban da Aka Sace a Borno Bayan Fiye da Wata Biyu

Fiye da wata biyu bayan sace ɗalibai daga makarantu uku da ke garin Mussa a Jihar Borno, har yanzu iyaye da iyalansu na ci gaba da jiran ganin an kuɓutar da 'ya'yansu. Lamarin ya sake nuna irin ƙalubalen tsaro da Najeriya ke fuskanta, musamman yawaitar sace ɗalibai daga makarantu, duk da ƙoƙarin da gwamnati ta ce tana yi na magance matsalar tsaro. A cikin 'yan shekarun nan, masu garkuwa da mutane sun ƙara kai hare-hare kan makarantu a sassa daban-daban na ƙasar, lamarin da ke ci gaba da jefa ɗalibai da iyayensu cikin fargaba. A ranar 10 ga Yulin 2026 , gwamnatin tarayya ta sanar da ceto wasu ɗ

Matawalle Ya Yi Kira Ga 'Yan Adawa Su Guji Ayyukan da Ka Iya Bata Sunan Najeriya

Ƙaramin Ministan Tsaro, Bello Mohammed Matawalle , ya buƙaci 'yan adawa da su guji duk wani abu da ka iya tunzura al'umma ko kuma ɓata sunan Najeriya a idon ƙasashen duniya. A cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Ahmad Dan-Wudil , ya fitar, Matawalle ya ce abin takaici ne kan zargin da ake yi cewa tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar , ya ɗauki hayar wasu kamfanonin ƙasashen waje domin yaɗa tsofaffin takardu da suka shafi Shugaba Bola Ahmed Tinubu a Amurka. Ministan ya ce, idan har zargin gaskiya ne, irin wannan mataki ba ya amfani ga dimokuraɗiyyar Najeriya, kuma ba ya taim

Damina da Wahalar Hanya Su Ne Babban Kalubale Yayin da 'Yan Ta'adda Suka Tsere Zuwa Dazuka

Kwamandan Rundunar Haɗin Gwiwa ta Operation FANSAN YAMMA a Arewa maso Yamma, Manjo Janar W.B. Idris , ya bayyana cewa hare-haren sojoji da ake ci gaba da kai wa sun tilasta wa 'yan ta'adda da masu garkuwa da mutane barin manyan hanyoyi tare da tserewa zuwa cikin dazuka da ƙauyuka masu nisa. Janar Idris ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da wakilan kafafen yaɗa labarai na fannin tsaro a Hedikwatar Operation FANSAN YAMMA da ke Gusau, Jihar Zamfara. Ya ce hare-haren da sojoji suka kai na tsawon watanni, tare da amfani da sahihan bayanan sirri da sintiri a yankunan da ake fama da matsalar t

Dakarun Operation HADIN KAI Sun Kama Mutum Biyar da Ake Zargi da Garkuwa da Mutane a Yobe

Dakarun Sashe na 2 na Operation HADIN KAI (OPHK) tare da haɗin gwiwar Ƙungiyar Maharba ta Jihar Yobe sun kama wasu mutum biyar da ake zargi da aikata laifin garkuwa da mutane a wani samame da suka kai bisa sahihan bayanan sirri. An gudanar da samamen ne a ranar 23 ga Yulin 2026 a ƙauyen Jegalari da ke Ƙaramar Hukumar Fune a Jihar Yobe. Sanarwar ta ce dakarun Bataliya ta 233 da ke sansanin soji na Damaturu ne suka gudanar da aikin bayan samun sahihan bayanan sirri kan ayyukan waɗanda ake zargin. A yayin samamen, jami'an tsaro sun ƙwato bindigogi uku ƙirar AK-47 da aka ƙera a cikin gida , bindig

Gwamnatin Sokoto Ta Ayyana Juma'a Ranar Hutu Domin Yin Rajistar Katin Zaɓe

Gwamnatin Jihar Sokoto ta ayyana Juma'a, 24 ga Yulin 2026 , a matsayin ranar hutu ga ma'aikatan gwamnati domin ba su damar shiga aikin rajistar masu kaɗa ƙuri'a da kuma samun Katin Zaɓe na Dindindin (PVC) . Gwamnan jihar, Ahmed Aliyu , ya buƙaci dukkan ma'aikatan gwamnati da suka kai shekarun yin zaɓe amma ba su yi rajista ba, su yi amfani da wannan damar wajen yin rajista domin su sami damar cika haƙƙinsu na ɗan ƙasa a babban zaɓen da ke tafe. A cikin wata sanarwa da Darakta Janar na Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama'a na Gwamna, Abubakar Bawa , ya fitar, an bayyana cewa gwamnatin jihar na ci gab

Ƙungiyar Sadarwa ta Afirka Ta Amince da Sanarwar Abuja 2026 Kan Inganta Haɗin Intanet a Nahiyar

Ƙasashen mambobin Ƙungiyar Sadarwa ta Afirka (African Telecommunications Union – ATU) sun amince da Sanarwar Abuja ta 2026 kan Ingantacciyar Haɗin Intanet a Afirka (Abuja 2026 Declaration on Meaningful Connectivity) , a wani mataki da ke nuna sabon babi a tafiyar sauyin fasahar dijital a nahiyar. An cimma matsayar ne a yayin Taro na Bakwai na Wakilan Ƙasashen Mambobi (7th Ordinary Session of the Conference of Plenipotentiaries) da ke gudana a Abuja, inda aka tsara muhimman abubuwan da za su jagoranci ci gaban fasahar dijital a Afirka. Sanarwar ta mayar da hankali kan muhimman fannoni da suka h