Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da wani Kwamitin Haɗin Gwiwar Ma'aikatu domin tsara Dokar Gyaran Harajin Ƙarin Daraja (VAT Modification Order) ta shekarar 2026 , a wani muhimmin mataki na aiwatar da sabbin dokokin haraji na Najeriya.
Ministan Kuɗi kuma Ministan Kula da Tattalin Arziki, Taiwo Oyedele , ne ya rantsar da mambobin kwamitin, wanda aka ɗora wa alhakin nazarin tanade-tanaden da suka shafi kayayyaki da ayyukan da aka keɓe daga biyan VAT ko aka sanya musu harajin sifili (Zero-rated) ƙarƙashin Dokar Haraji ta Najeriya.
Ana kuma sa ran kwamitin zai gabatar da shawarwari kan yadda za a samar da tsari mafi sauƙi kuma mai inganci ga 'yan kasuwa da masu gudanar da harkokin haraji.
Kwamitin ya ƙunshi wakilai daga Ma'aikatar Kuɗi , Hukumar Tara Kuɗaɗen Shiga ta Najeriya (Nigeria Revenue Service) , Hukumar Kwastam ta Najeriya , Ma'aikatar Kasuwanci , Ƙungiyar Masana'antu ta Najeriya (MAN) , Kwamitin Ba da Shawara Kan Haraji , da kuma Tax Justice and Governance Platform .
An bai wa kwamitin wa'adin mako shida domin gabatar da daftarin dokar gyaran VAT, sabon jadawalin kayayyaki da ayyukan da za a keɓe daga haraji, tare da rahoton shawarwarin da aka tattara daga masu ruwa da tsaki.
