Kotun Sauraren Kararrakin Wasanni ta Duniya (CAS) ta sanya 8 ga watan Oktoba a matsayin ranar da za ta fara sauraren ƙarar da Senegal ta ɗaukaka kan hukuncin da ya ƙwace mata kofin gasar AFCON 2025 .

Tun farko, Senegal ce ta doke Morocco da ci 1-0 a wasan ƙarshe na gasar da aka kammala a watan Janairu. Sai dai daga bisani Hukumar Kwallon Kafa ta Afirka (CAF) ta sauya hukuncin, tare da ayyana Morocco a matsayin zakara bayan ta bai wa Senegal hukuncin shan kashi da ci 3-0 .

Lamarin ya samo asali ne bayan 'yan wasan Senegal sun fice daga filin wasa sakamakon rashin amincewa da fenaritin da aka bai wa Morocco a ƙarshen wasan, yayin da ake kunnen doki babu ci.

Bayan an dakatar da wasan na tsawon mintuna 17 , 'yan wasan Senegal sun dawo filin, amma ɗan wasan Morocco Brahim Diaz ya kasa cin fenaritin.

A ranar 25 ga Maris , Senegal ta shigar da ƙara a gaban Kotun CAS tana neman a soke hukuncin CAF tare da mayar mata da kofin da ta ce ta lashe a filin wasa.

Yanzu dai ana sa ran sauraren ƙarar zai gudana ne a ranar 8 ga Oktoba , inda za a yanke hukunci kan wannan takaddama mai ɗaukar hankali a fagen ƙwallon ƙafar Afirka.