Rahotanni da dama daga Amurka sun bayyana cewa Shugaban ƙasar, Donald Trump, ya yanke shawarar dakatar da ƙara faɗaɗa hare-haren sojin Amurka kan Iran, aƙalla a halin yanzu.

A cewar rahotannin, Trump ya ɗauki wannan mataki ne a ranar Juma'a bayan wasu manyan jami'an gwamnati sun nuna damuwa kan raguwar makamai masu linzami na kariya na Patriot , waɗanda ke da tsadar gaske, tare da fargabar cewa ci gaba da hare-haren na iya janyo rashin jituwa tsakanin Amurka da ƙawayenta na ƙasashen Larabawa da ke yankin Tekun Fasha.

Sai dai har zuwa yanzu, babu wata sanarwa a hukumance da Fadar White House ta fitar da ke tabbatar da dakatar da hare-haren. Duk da haka, Fadar White House ta bayyana cewa Shugaba Trump na fifita warware rikice-rikice ta hanyar tattaunawa da diflomasiyya.

Rahotannin sun kuma nuna cewa daren Juma'a shi ne karo na farko cikin kusan makonni biyu da ba a kai hare-haren sama na Amurka kan Iran ba. Haka kuma, ba a samu irin waɗannan hare-hare ba a daren Asabar.

Sai dai har yanzu babu tabbacin ko wannan mataki na nufin kawo ƙarshen hare-haren gaba ɗaya, ko kuwa dakatarwa ce ta wucin gadi yayin da ake ci gaba da tantance halin da ake ciki.