Yara sama da miliyan ɗaya sun koma makaranta cikin watanni 20 – Ministan Ilimi
Ministan Ilimi na Najeriya, Maruf Tunji Alausa, ya ce sama da yara miliyan ɗaya da ba sa zuwa makaranta sun koma ajujuwa cikin watanni 20 da suka gabata. Ministan ya kuma ce kusan ’yan mata miliyan 6.7 sun amfana da shirye-shiryen gwamnati da aka ƙaddamar domin ƙara yawan yaran da ke shiga makaranta da kuma rage yawan waɗanda ke barin karatu. Alausa ya bayyana hakan ne a Abuja yayin da yake karɓar wakilin UNESCO a Najeriya, Farfesa Isaiah Barreto Da Rosa, wanda ya kai masa ziyara. Ministan ya buƙaci ƙara haɗin gwiwa tsakanin Ma’aikatar Ilimi da UNESCO domin tallafa wa shirin gwamnatin Shugaba
