Rundunar Kare Juyin Juya Halin Iran, IRGC , ta yi iƙirarin cewa ta kai hari kan jiragen ruwan yaƙin Amurka guda biyu da makamai masu linzami.

A cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar a safiyar Laraba, ta ce rundunar ta kai harin ne kan jiragen DDG-119 da DDG-53 , waɗanda ke ɗauke da makamai masu linzami da tsarin kariya na Aegis .

IRGC ta yi iƙirarin cewa makaman da ta harba sun yi wa jiragen ruwan babban lahani .

Sai dai rahotannin da suka fito daga ɓangaren Amurka sun ce jiragen ruwan Amurkan sun yi nasarar kauce wa hare-haren makamai masu linzami da Iran ta kai, ba tare da wani jami’in sojan Amurka ya ji rauni ba.

Hakan na zuwa ne bayan da Rundunar Tsakiyar Sojin Amurka, CENTCOM , ta sanar da lalata tankokin ɗanyen man Iran guda biyar a ranar Talata, a matsayin martani ga hare-haren makamai masu linzami da IRGC ta kai kan wani jirgin ruwan yaƙin Amurka.

Ci gaba da musayar hare-haren na ƙara tsananta rikicin tsakanin Iran da Amurka, tare da ƙara barazana ga tsaron zirga-zirgar jiragen ruwa da jigilar makamashi a yankin mashigar Hormuz .