Kotun Ɗaukaka Ƙara ta Najeriya ta tabbatar da hukuncin ɗaurin shekaru 490 a gidan yari da aka yanke wa tsohon Manajan Daraktan Bankin Shige da Fitar da Kayayyaki na Najeriya (NEXIM Bank), Robert Orya .
Kotun ta same shi da laifi kan tuhume-tuhume 49 , inda aka yanke masa hukuncin shekaru 10 a kan kowace tuhuma, wanda ya kai jimillar shekaru 490. Sai dai kotun ta bayyana cewa za a yi zaman gidan yarin a lokaci guda , ba ɗaya bayan ɗaya ba.
Orya ya shugabanci NEXIM Bank daga shekarar 2009 zuwa 2016 . A lokacin da yake kan mukamin ne aka sake naɗa shi a shekarar 2014 a zamanin gwamnatin tsohon Shugaba Goodluck Jonathan.
Bayan barin mukaminsa, Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Najeriya, EFCC, ta gurfanar da shi a gaban kotu a shekarar 2021 , bisa tuhume-tuhume 49 da suka haɗa da zargin karɓar kuɗi ta hanyar yaudara da sauran laifukan da suka shafi kuɗaɗen da suka kai kimanin naira biliyan 2.4 .
A ranar 5 ga Fabrairu, 2026 , Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta same shi da laifi, tare da yanke masa hukuncin ɗaurin shekaru 490.
A hukuncin da kwamitin alkalai uku na Kotun Ɗaukaka Ƙara ya yanke, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Muhammed Danjuma , kotun ta ce alkalin kotun farko, Mai Shari’a Messiri , ya yi daidai wajen yanke hukuncin.
Mai Shari’a Danjuma, tare da sauran alkalan biyu, Ntong Ntong da Ele Enenche , sun ce masu gabatar da ƙara sun samu nasarar tabbatar da tuhumar da ake yi wa Orya ba tare da wata tantama mai ma’ana ba .
