Za mu ɗaukaka ƙara kan hukuncin hana saka hijabi a makarantar Ibadan - MURIC
Ƙungiyar kare haƙƙoƙin Musulmi ta MURIC ta bayyana cewa ba ta amince da hukuncin Kotun Ɗaukaka Ƙara da ta soke hukuncin da ya bai wa ɗalibai mata Musulmi damar sanya hijabi a makarantar International School, Jami'ar Ibadan (ISI) . A cikin wata sanarwa, MURIC ta ce za ta ɗaukaka ƙara zuwa Kotun Koli, tana mai cewa hukuncin kotun ɗaukaka ƙarar ya ƙunshi kura-kurai na shari'a. Ƙungiyar ta kuma bayyana cewa ta riga ta shigar da takardar ɗaukaka ƙara tare da buƙatar dakatar da aiwatar da hukuncin har sai Kotun Koli ta yanke hukunci na ƙarshe. Wannan mataki ya biyo bayan hukuncin da Kotun Ɗaukaka Ƙa
