Wasu fitattun jaruman Kannywood na ci gaba da sanar da ficewarsu daga ƙungiyar Triple R Kannywood for Renewed Hope , wadda aka kafa domin tallata manufofin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da jam'iyyar APC gabanin babban zaɓen shekarar 2027.
Na baya-bayan nan da ya sanar da ficewarsa shi ne fitaccen jarumi Rabiu Rikadawa , wanda ya ce ya ɗauki matakin ne saboda abin da ya bayyana a matsayin rashin tabbas da kuma rashin bin dokoki da ƙa'idojin ƙungiyar .
A cewar Rikadawa, yadda ake tafiyar da harkokin ƙungiyar bai dace da abin da aka kafa ta a kai ba, lamarin da ya sa ya yanke shawarar ficewa.
Kafin sanarwar tasa, wasu fitattun jaruman Kannywood sun riga sun fice daga ƙungiyar, ciki har da Mansura Isa , fitaccen marubuci Ibrahim Birniwa , da kuma jarumi Yusuf Sasen .
Ficewar waɗannan fitattun mambobi ta haifar da ce-ce-ku-ce a cikin masana'antar Kannywood da kuma tsakanin masu bibiyar harkokin siyasa, yayin da ake ci gaba da shirye-shiryen tunkarar zaɓen 2027.
Sai dai har yanzu shugabannin ƙungiyar Triple R Kannywood for Renewed Hope ba su fitar da wata sanarwa a hukumance ba dangane da ficewar mambobin nata.
