Rundunar ’yan sandan jihar Borno da ke arewa maso gabashin Nijeriya ta kama mutum 103 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban, ciki har da ta’ammali da miyagun ƙwayoyi, sayar da su da kuma riƙe makamai ba bisa ƙa’ida ba.
An gudanar da aikin ne tsakanin ranar 29 ga Oktoba da 2 ga Nuwamba, 2026, a birnin Maiduguri da wasu yankunan jihar.
A cikin wata sanarwa da Jami’in Hulɗa da Jama’a na rundunar, ASP Nahum Daso, ya sanya wa hannu, wadda aka wallafa a shafin rundunar na X ranar Talata, rundunar ta bayyana aikin a matsayin wani gagarumin nasara a ƙoƙarin da take yi na kawar da masu aikata laifuka.
Ya ce aikin ya haɗa da jami’an ’yan sanda da sauran hukumomin tsaro, waɗanda suka gudanar da samame da sintiri a wuraren da aka fi samun ayyukan laifuka da matsalolin tsaro.
Daga cikin wuraren da aka gudanar da aikin akwai Gwange, Santiago, Texaco, Ajari, Gadan Zare, Budum, Shehuri, Bulabulin, Abbaganaram, Baga Road, Gidan Dambe, UNIMAID 202 Housing Estate, Mairi Kuwait, Bakari, Zanneri, Polo, Giwa Barrack Area, Kwanan Yobe, Jiddari, Kaleri, Damboa Road, Circular da Moduganari.
A cewar Daso, an kama waɗanda ake zargin bisa zarge-zargen damun jama’a, ta’ammali da miyagun ƙwayoyi, sayar da su da kuma mallakar makamai masu haɗari.
Ya ƙara da cewa jami’an tsaron sun ƙwace nau’o’in miyagun ƙwayoyi har guda 11 yayin samamen.
Rundunar ta ce za ta ci gaba da gudanar da sintiri da samame domin ƙarfafa tsaro da kare rayuka da dukiyoyin al’umma a jihar.
