’Yan bindiga sun kashe mutum 12 ’yan gida ɗaya bayan sun cinnawa gidansu wuta a wani hari da suka kai ƙauyen Gidan Taba da ke Ƙaramar Hukumar Maradun ta Jihar Zamfara, a arewa maso yammacin Najeriya.

Kafofin watsa labaran ƙasar, ciki har da Daily Trust, The Punch, Premium Times da Vanguard, sun ruwaito cewa harin ya faru ne da misalin ƙarfe 10 na daren ranar Asabar.

Rahotanni sun ce maharan sun kai hari gidan wani mutum mai suna Mallam Muhammadu Sani, inda suka yi garkuwa da mutum bakwai.

Mazauna ƙauyen sun bayyana cewa mutane 13 da ke cikin gidan, ciki har da matan Muhammadu Sani biyu, ’ya’yansa shida, matar ƙaninsa da ’ya’yansu uku, sun buya a wani ɗaki domin guje wa sace su.

Sai dai bayan maharan sun buƙaci waɗanda ke cikin ɗakin su buɗe ƙofa, amma suka ƙi, sai suka cinna wa ɗakin wuta.

Rahotanni sun ce matar ƙanin Muhammadu Sani ce kaɗai ta tsira, yayin da sauran mutum 12 suka mutu sakamakon gobarar.

Sai dai kwamishinan ’yan sandan Jihar Zamfara ya tabbatar da faruwar harin, amma ya ce adadin waɗanda suka mutu mutum 11 ne, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Daga bisani, an gudanar da jana’izar waɗanda suka mutu a ranar Lahadi.

Harin na Gidan Taba shi ne na baya-bayan nan cikin jerin hare-haren ’yan bindiga a Ƙaramar Hukumar Maradun ta Jihar Zamfara.

A makon da ya gabata ma, wasu ’yan bindiga sun yi wa jami’an tsaro kwanton ɓauna a Gidan Kano, da ke kan hanyar Gusau zuwa Sokoto.

Jami’an tsaron na cikin wata motar bas mai ɗaukar mutum 18 ta Hukumar Sufurin Jihar Zamfara, inda suke aikin samar da tsaro yayin gudanar da sake zaɓen fidda gwani na jam’iyyar APC a mazaɓar Zamfara ta Arewa.

Rahotanni sun ce jami’an tsaro biyar ne suka rasa rayukansu a wannan kwanton ɓauna.