An ƙaddamar da shirin ne ƙarƙashin wani tsari mai suna Spark, wanda Hukumar Ba da Lamunin Kuɗi ga Masu Amfani ta Najeriya (Nigerian Consumer Credit Corporation), wadda aka fi sani da CrediCorp, ke gudanarwa.

An ƙaddamar da shirin ne ƙarƙashin wani tsari mai suna Spark, wanda Hukumar Ba da Lamunin Kuɗi ga Masu Amfani ta Najeriya (Nigerian Consumer Credit Corporation), wadda aka fi sani da CrediCorp, ke gudanarwa.

Shirin zai bai wa ’yan Najeriya damar neman rance ta amfani da lambobin USSD, ba tare da buƙatar mallakar wayar zamani ko sayen kunshin intanet ba.

Domin cin gajiyar shirin, an bayyana cewa masu buƙata za su iya amfani da lambar 347333# ta wayoyinsu.

A cewar hukumar, shirin zai kuma bai wa mutanen da ba su taɓa karɓar rance a baya ba damar samun lamuni, ta yadda za su fara amfani da tsarin karɓar bashi da kuma gina tarihin amincin biyan basussuka a ƙasar.

Ga matakai guda takwas da za ku bi domin neman rancen:

Danna lambar *5120# a wayarka domin fara rajista.

Amince da sharuɗɗa da ƙa'idojin shirin.

Shigar da lambobi huɗu na ƙarshe na lambar BVN ɗinka.

Ƙirƙiri PIN mai lambobi huɗu da za ka riƙa amfani da shi wajen shiga ko gudanar da ayyuka ta hanyar USSD.

Zaɓi nau'in rancen kuɗin da kake buƙata.

Karanta sharuɗɗa da ƙa'idojin shirin, sannan ka amince da su.

Bi umarnin da aka nuna a wayarka domin haɗa bayanan asusun bankinka.

Bayan kammala matakan, za ka karɓi saƙon tabbatarwa a wayarka, sannan a tura maka kuɗin rancen cikin mintuna biyu zuwa biyar, kamar yadda bayanin shirin ya nuna.

Waɗanne mutane ne suka cancanci samun rancen?

Bisa ga bayanan da aka bayar kan shirin, waɗannan su ne wasu daga cikin sharuɗɗan cancantar samun rancen:

Dole ne mutum ya kasance ma'aikacin gwamnatin jiha ko ta tarayya, ko kuma yana aiki a fannin koyarwa ko aikin soja.

Dole ne shekarunsa su kasance tsakanin 22 zuwa 58.

Ana buƙatar ya gabatar da takardar shaidar tabbatar da cewa ba shi da matsalar bashi daga hukumar kula da tarihin bashi da aka amince da ita.

Dole ne ya kasance yana da Lambar Tabbatar da Asusun Banki (BVN).

Dole ne ya kasance ya shafe aƙalla watanni uku yana aiki.

Kamfanin ko hukumar da yake aiki a cikinta dole ne ta kasance cikin waɗanda aka amince da su domin shiga shirin.

CrediCorp za ta tantance yawan kuɗin da mai neman rancen ke kashewa wajen biyan buƙatunsa na wata-wata domin tantance cancantarsa da adadin rancen da zai iya samu.

Lura: Ana buƙatar masu sha'awar shirin su tabbatar da sahihancin bayanan da matakan neman rancen ta hanyar CrediCorp kafin fara rajista. Kada ku bayyana cikakkun bayanan BVN ko PIN ɗinku ga wani mutum ko shafin intanet da ba ku tabbatar da sahihancinsa ba.