Kakakin shugaban ƙasar, Bayo Onanuga, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa, inda ya ce an tsara gudanar da bikin ƙaddamar da aikin a ranar 3 ga Disamba.
Aikin layin dogon mai tsawon kilomita 203, wanda ya haɗa Kaduna, Zaria da Kano, ya kai kusan kashi 90 cikin 100 na kammaluwa.
Haka kuma, aikin layin dogo mai tsawon kilomita 400 daga Kano zuwa Katsina da Maradi ya kai kashi 70 cikin 100 na kammaluwa.
Sabon layin dogon Kaduna zuwa Kano, wanda yake ƙarin wani ɓangare ne na layin dogon Abuja zuwa Kaduna, zai samar da haɗin sufuri ta jirgin ƙasa tsakanin Abuja, Kaduna, Zaria da Kano.
Ana kuma sa ran aikin zai ƙarfafa zirga-zirgar fasinjoji da kayayyaki tsakanin manyan cibiyoyin kasuwanci a Arewacin Najeriya.
A baya-bayan nan, wata tawagar gwamnatin tarayya ƙarƙashin jagorancin Babban Sakataren Ma’aikatar Sufuri ta Tarayya, Injiniya Funso Adebiyi, ta gudanar da aikin duba layukan dogon biyu bisa umarnin Shugaba Tinubu.
Tawagar ta bayyana gamsuwarta da ingancin aikin, musamman wajen shimfiɗa layukan dogo, gina magudanan ruwa, kare tuddan layin dogo, shimfiɗa duwatsu da kuma daidaita ƙasa.
Binciken ya kuma ƙunshi gwajin tafiyar jirgin ƙasa daga Jaji da ke Jihar Kaduna zuwa Kano, domin bai wa jami’an damar tantance ingancin layin dogon da sauran abubuwan more rayuwa da aka tanada.
