Shugaban Ma'aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Femi Gbajabiamila, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba.

Gbajabiamila, wanda ke jagorantar kwamitin shugaban ƙasa kan kafa 'yan sandan jihohi, ya ce masu ba shugaban ƙasar shawara kan harkokin Majalisar Dattawa da ta Wakilai, Sanata Basheer Lado da Dakta Wasiu Olanrewaju-Smart, ne suka miƙa masa kudirin a hukumance.

Ya ce dukkan majalisun dokokin jihohi 36 na Najeriya sun amince da kudirin, lamarin da ya cika sharuɗɗan da kundin tsarin mulkin ƙasar na 1999 ya tanada a sashe na 9(2), wanda ke buƙatar amincewar aƙalla majalisun dokokin jihohi 24, wato kashi biyu bisa uku na jihohi 36.

Gbajabiamila ya ce: “Shugaba Tinubu zai nazarci kudirin gyaran kundin tsarin mulkin tare da tuntubar Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya. Zai kuma sanya hannu a kansa a wani bikin sanya hannu na musamman.”

Shugaban Ma'aikatan Fadar Shugaban Ƙasar ya kuma bayyana cewa kwamitin shugaban ƙasa kan kafa 'yan sandan jihohi, tare da tallafin kwamitin ba da shawarwari kan manufofi, ya kammala tattaunawa mai zurfi da masu ruwa da tsaki, da kuma shawarwarin da aka gudanar a faɗin ƙasar, domin samar da daftarin kudirin dokar 'yan sanda ta ƙasa.