Uwargidan shugaban ƙasar, Sanata Oluremi Tinubu, ce ta sanar da bayar da kyaututtukan a wani taro da aka gudanar a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.

Haka kuma, an ware naira miliyan 100 ga babban mai horar da ƙungiyar, yayin da kowane mamba na tawagar masu horarwa da sauran ma'aikatan ƙungiyar zai karɓi naira miliyan 50.

Sanata Oluremi Tinubu ta yabawa ƴan wasan bisa wannan gagarumar nasara, musamman yadda suka samu nasarar lashe wasanni shida a jere, tare da nuna ladabi da girmamawa bayan kammala wasan ƙarshe.

Ta bayyana cewa nasarar za ta zama abin ƙarfafawa ga sauran matasa mata a Najeriya, tare da nuna musu cewa za su iya cimma manyan manufofinsu har a matakin duniya.

Ta kuma yaba wa masu horar da ƙungiyar da magoya bayan da suka bayar da gudunmawa wajen samun nasarar.

Tawagar Flamingos ta samu nasarar lashe kofin duniya na mata ƴan ƙasa da shekara 17 a karon farko a tarihinta, bayan doke Japan da ci 2-1 a wasan ƙarshe da aka buga ranar 7 ga Nuwamban 2026.