’Yan wasan sun sauka a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe da ke Abuja, babban birnin Najeriya, da safiyar ranar Litinin.
A ranar Asabar ne tawagar ta lashe kofin duniya bayan ta doke takwararta ta Japan da ci 2-1 a wasan ƙarshe na gasar da aka gudanar a ƙasar Morocco.
Tawagar ta samu tarba daga dimbin magoya baya da suka taru a filin jirgin saman domin taya ’yan wasan murnar nasarar da suka samu.
Ana sa ran tawagar za ta wuce kai tsaye zuwa fadar shugaban ƙasa, inda aka shirya musu tarba ta musamman.
Wannan ne karon farko da Najeriya ta lashe gasar cin kofin duniya ta mata ’yan ƙasa da shekara 17, lamarin da ya kafa sabon tarihi a ƙwallon ƙafar ƙasar.
