A cikin bidiyon da ya yaɗu a shafukan sada zumunta, an ga jami'an sojoji da na DSS suna ganawa da wasu ƴanbindiga masu riƙe da makamai a tsakiyar wani daji.

Tun bayan yaɗuwar bidiyon, mutane na ta tambayar dalilin da ya kai jami'an tsaro cikin daji da kuma abin da suka tattauna da ƴanbindigar.

Sai dai a cikin wata sanarwa da rundunar sojin ta fitar, ta ce jami'anta sun je dajin ne a wani yunƙuri na sulhu tsakanin ƴanbindigar da jami'an tsaro a jihar Kwara.

Sanarwar ta ce: "Hedikwatar JTF OPSS na son fayyace cewa abin da aka gani a bidiyon wani tsararren matakin tsaro ne da ya shafi sojoji da wasu ƴanbindiga da suka nuna aniyarsu ta miƙa makamansu tare da taimakawa wajen sakin mutanen da suka yi garkuwa da su."

Rundunar ta ƙara da cewa a yayin ganawar, sojojin sun samu nasarar karɓar bindigogi kirar AK-47 guda 12, yayin da ƴanbindigar suka saki mutum 10 da suka yi garkuwa da su.