Gwamnan ya bayyana hakan ne a yayin wani liyafar cin abincin dare ta musamman da ya shirya wa ‘yan wasan a jihar Legas, domin taya su murnar nasarar da suka samu tare da yaba musu bisa ƙoƙarin da suka yi.
Baya ga ‘yan wasan, gwamnan ya kuma bai wa kowane ɗaya daga cikin masu horas da tawagar kyautar naira miliyan 10 da wayar iPhone, tare da wasu kyaututtuka.
Wannan na zuwa ne bayan Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya bai wa kowace ‘yar wasa kyautar naira miliyan 100, sakamakon nasarar da suka samu a ƙasar Morocco.
Haka kuma, Majalisar Dattawan Najeriya ta bai wa kowace daga cikin ‘yan wasan kyautar naira miliyan 100.
Tawagar Flamingos ta Najeriya ta kafa tarihi a matsayin tawagar Afirka ta farko da ta lashe gasar cin kofin duniya ta mata ‘yan ƙasa da shekaru 17, bayan ta doke takwararta ta Japan da ci 2-1 a wasan ƙarshe da aka gudanar a Morocco.
