Shigowar Diallo takarar na zuwa ne a wani lokaci mai muhimmanci, bayan tsohon kocin Arsenal, Arsène Wenger, wanda shi ma ɗan Faransa ne, ya ƙi amincewa da shiga takarar domin ƙalubalantar Infantino.

Diallo, wanda shi ne shugaban Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Faransa (FFF), ya ce zai nemi haɗin gwiwa da wani ɗan takara daga Japan, Kozo Tashima, mamba a kwamitin FIFA kuma tsohon shugaban Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Japan.

A ranar Talata, 17 ga Nuwamba, Diallo ya tabbatar da cewa zai nemi haɗin gwiwar Tashima domin kauce wa rarrabuwar ƙuri'un masu adawa da Infantino.

“Idan muna son yin nasara, na yi imanin dole ne mu haɗa ƙarfi wuri guda,” in ji Diallo yayin wata ganawa da 'yan jarida a birnin Paris.

Diallo mai shekaru 63 ya ce bai yi niyyar shiga takarar ba tun farko, sai dai kwamitin zartarwa na Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Turai (UEFA) ne ya buƙace shi da ya tsaya takara ranar Litinin, sannan Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Faransa ta amince da hakan baki ɗaya.

Damar kayar da Infantino

Gianni Infantino ya fuskanci suka a duniyar ƙwallon ƙafa kan wasu matakai da ya ɗauka wajen gudanar da harkokin FIFA, ciki har da ƙirƙirar kyautar zaman lafiya ta FIFA, wadda ya bai wa Shugaban Amurka, Donald Trump, a shekarar 2025.

Haka kuma, an zargi Infantino da yin katsalandan wajen ɗage dakatarwar da aka yi wa ɗan wasan tawagar Amurka, Folarin Balogun, yayin gasar Kofin Duniya, bayan Trump ya kira shi ta waya.

A watan Yulin da ya gabata, Infantino ya dakatar da wani shiri na sayar da hannun jarin kashi 20 cikin 100 na kamfanin kasuwanci na FIFA, FIFA Forward Enterprise, wanda darajarsa ta kai dala biliyan 4.2. Batun ya haifar da rashin jituwa tsakanin FIFA da wasu ƙasashen Turai.

Infantino na shirin neman wa'adi na huɗu a matsayin shugaban FIFA, kuma yana samun goyon bayan hukumomin ƙwallon ƙafa na Afirka (CAF) da Kudancin Amurka (CONMEBOL).

Masu sharhi kan zaɓen FIFA sun shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa, duk da cewa UEFA na da ƙuri'u 55 daga cikin ƙuri'u 211 na zaɓen, Diallo ba shi da cikakken goyon bayan dukkan ƙasashen Turai.

Ana sa ran rufe karɓar sunayen 'yan takarar shugabancin FIFA a ranar Laraba, kafin a tantance su zuwa ranar 18 ga Fabrairun 2027.

Za a gudanar da zaɓen ne a birnin Rabat na ƙasar Morocco, ranar 18 ga Maris ɗin 2027.