A cikin wata sanarwa da hukumar ta wallafa a shafinta na X, NiMet ta ce ana sa ran samun yanayi mai zafi tun daga safiyar ranar a faɗin yankin.
Sanarwar ta bayyana cewa zafin zai ƙara tsananta yayin da rana ke ƙara ɗaukaka, kuma zai ci gaba har zuwa yammacin ranar.
Dangane da wannan hasashe, hukumar ta shawarci mazauna yankin da su guji zama ko yin ayyuka a ƙarƙashin zafin rana kai tsaye domin rage haɗarin kamuwa da matsalolin da zafin rana ke haifarwa.
Haka kuma, ana shawartar al'umma da su riƙa shan ruwa akai-akai, sanya tufafi masu sauƙi da kuma neman inuwa a lokutan da zafin rana ya fi tsanani.
