Daraktar da ke kula da ofishin Babban Sakataren Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya, Dr Folake Olatunji-David, ce ta bayyana hakan a Abuja, yayin taro na 37 na Kwamitin Dindindin na Ƙasa kan tantance takardun shaidar karatu daga ƙasashen waje.

Ta bayyana buƙatar ƙarfafa hanyoyin tantance takardun shaidar karatu, tare da tabbatar da cewa waɗanda ke shirin yi wa ƙasa hidima ta shirin NYSC sun halarci makarantun da suka bayar da takardun shaidar kammala karatunsu.

Dr Olatunji-David ta ce ma’aikatar ta ƙaddamar da tsarin tantance takardun shaidar karatu na Nijeriya da na ƙasashen waje ta hanyar amfani da fasahar zamani tun farkon shekarar nan, wanda ya taimaka wajen inganta gaskiya, inganci da saurin gudanar da ayyukan tantancewa.

Ta ƙara da cewa kwamitin zai kuma duba hanyoyin sa ido kan ’yan Nijeriya da ke karatu a makarantun ƙasashen Afirka, da kuma amincewa da hukumomin da ke kula da ilimi a ƙasashen waje a matsayin sahihan wuraren tabbatar da takardun shaidar karatu.

Haka kuma, kwamitin zai tsara ƙa’idojin tantance kwatankwacin takardun shaidar kammala karatun sakandare daga ƙasashen waje.

Sauran batutuwan da za a tattauna sun haɗa da yadda makarantun da ke aiki a Nijeriya bisa tsarin karatun ƙasashen waje ke bin manufofin ilimin ƙasar, da kuma tsarin bayar da wasiƙar rashin ƙin amincewa ga makarantun da abin ya shafa.

Ma’aikatar ta jaddada aniyarta ta ƙarfafa tsarin tantancewa da sa ido, domin tabbatar da cewa takardun shaidar karatu daga makarantun da aka amince da su ne kawai ake karɓa a hukumance.

Wata sanarwa da Daraktar Watsa Labarai da Hulɗa da Jama’a ta ma’aikatar, Boriowo Folasade, ta fitar ranar Litinin, ta ambato Dr Olatunji-David tana jaddada cewa bai kamata ingancin karatun da ake yi a ƙasashen waje ya kasance ƙasa da matakin da hukumomin Nijeriya za su amince da shi ba.