Hukumar ta bayyana cewa mutanen da ake bibiyarsu sun haɗa da ma’aikatan jinya, masu aikin gida da kuma mijin matar.
A cikin rahoton da ta fitar ranar 24 ga Oktoba, 2026, NCDC ta ce an kuma samu rahoton wani da ake zargin ya kamu da cutar a Jihar Ribas a ranar 23 ga Oktoba, amma sakamakon gwaji ya tabbatar da cewa ba shi da cutar Ebola.
Rahoton ya ce matar da aka tabbatar ta kamu da cutar mai shekara 42 ce, wadda ta dawo Najeriya daga Uganda ta hanyar Addis Ababa a ranar 3 ga Oktoba, 2026, ta jirgin da ya isa Abuja daga ƙasashen waje.
A cewar hukumar, matar ta fara nuna alamun cutar kwanaki huɗu bayan shigowarta Najeriya. Ta fara zuwa wani asibiti mai zaman kansa a ranar 10 ga Oktoba, sannan ta sake zuwa wani asibiti a ranar 11 ga Oktoba, inda aka kwantar da ita domin samun kulawar likitoci.
NCDC ta ce an sanar da ita game da majinyaciyar a ranar 19 ga Oktoba, bayan haka aka gudanar da bincike tare da ɗaukar samfurin jininta domin gwaji. A ranar 20 ga Oktoba ne aka tabbatar da cewa tana ɗauke da cutar Ebola.
Alamomin da majinyaciyar ta nuna sun haɗa da zazzaɓi, gudawa, ciwon jiki da kuma ciwon maƙogwaro. Rahoton ya ce ba a samu rahoton zubar jini ba.
Darakta Janar na NCDC, Dr. Jide Idris, ya ce Gwamnatin Tarayya, ta hannun Ma’aikatar Lafiya da Jin Daɗin Jama’a, NCDC, hukumomin lafiya na Babban Birnin Tarayya Abuja da abokan hulɗa, suna ɗaukar matakan da suka dace domin shawo kan lamarin.
Ya bayyana cewa za a ci gaba da bibiyar mutanen da suka yi mu’amala da majinyaciyar na tsawon kwanaki 21 daga ranar da suka haɗu da ita, domin gano duk wanda ka iya fara nuna alamun cutar.
Dr. Idris ya jaddada cewa yin mu’amala da wanda ya kamu da Ebola ba yana nufin cewa mutum ya kamu da cutar ba. Ya kuma yi kira ga jama’a da su ba jami’an lafiya haɗin kai idan suka tuntube su domin gudanar da bibiyar lafiyarsu.
