Darakta Janar ta hukumar, Binta Bello, ce ta bayyana hakan a yayin taron tuntuba na 29 na masu ruwa da tsaki kan yaƙi da safarar mutane a Nijeriya, da kuma taron tsara manufofi na uku da aka gudanar a Abuja.
A cikin wata sanarwa da NAPTIP ta wallafa a shafinta na Facebook ranar Talata, Bello ta ce hukumar ta kuma karɓi tare da kula da mutane 2,700 da safarar mutane ta shafa a wannan lokacin.
Ta ƙara da cewa an gurfanar da mutane 85 a gaban kotu a ƙarƙashin shari’o’i 65, yayin da shari’o’i 74 suka haifar da samun mutane 97 da laifin safarar mutane.
Darakta Janar ɗin ta bayyana cewa tun bayan kafa hukumar, NAPTIP ta ceto mutane 28,762 tare da tabbatar da hukunta mutane 857 bisa laifukan safarar mutane.
Ta ce hukumar ta ƙara zafafa ƙoƙarinta wajen amfani da fasaha don yaƙi da safarar mutane, musamman ta intanet, da sauran hanyoyin cin zarafi da amfani da mutane ba bisa ƙa’ida ba.
Bello ta kuma bayyana cewa hukumar na ƙarfafa tattara bayanan sirri, kare waɗanda safarar mutane ta shafa da kuma haɗin gwiwa da ƙasashen duniya domin magance matsalar.
Ta yi kira da a ɗauki matakin gaggawa na kafa rundunar NAPTIP a Jihar Delta, wadda ta bayyana a matsayin jiha ɗaya tilo da har yanzu ba ta da rundunar hukumar.
A cewarta, kafa rundunar zai taimaka wajen ƙarfafa ayyukan hukumar da kuma inganta kariya ga waɗanda safarar mutane ta shafa a jihar.
A wani ɓangare kuma, Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta sake tabbatar da aniyarta ta ƙarfafa yaƙi da safarar mutane ta hanyar inganta tallafin hukumomi, goyon bayan manufofi da samar da isassun kuɗaɗe ga NAPTIP da sauran masu ruwa da tsaki.
Antoni Janar kuma Ministan Shari’a na ƙasar, Lateef Fagbemi, SAN, ne ya bayyana hakan yayin buɗe taron.
Ministan, wanda Muƙaddashin Daraktan Sashen Haƙƙin Bil Adama na Ma’aikatar Shari’a, Kabiru Haliru, ya wakilta, ya yaba wa NAPTIP da abokan aikinta bisa nasarorin da suka samu wajen gurfanar da masu safarar mutane, ceto waɗanda abin ya shafa, kula da su, wayar da kan jama’a da kuma samar da manufofin yaƙi da safarar mutane.
Ya jaddada buƙatar samun jajircewar siyasa mai ɗorewa, ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin hukumomi da samar da isassun kayan aiki domin samun nasara wajen yaƙi da safarar mutane a Nijeriya.
