Bincike ya gano cewa waɗanda ake zargin sun ƙware wajen safarar miyagun ƙwayoyi tsakanin ƙasashe, inda suke jigilar hodar iblis daga birnin Legas zuwa Kano, sannan su bi ta Jamhuriyar Nijar zuwa Libya, kafin su wuce Turai.

Bayan cafke su, hukumar ta ƙwace ƙullin hodar iblis guda 634, waɗanda nauyinsu ya kai kusan kilogiram 14.

A cikin wata sanarwa da ta fitar, NDLEA ta ce ta kama mutanen takwas ne a ranakun 30 da 31 ga watan Oktoban da ya gabata.

A wani rahoto da hukumar ta fitar, ta ce daga watan Janairun 2025 zuwa Satumban 2026, ta yi nasarar cafke mutane sama da 38,000 tare da ƙwace miyagun ƙwayoyi masu nauyin kusan kilogiram miliyan shida.

Hukumar ta ƙiyasta darajar ƙwayoyin da ta ƙwace aƙalla Naira tiriliyan 2.5, lamarin da ke nuna girman matsalar safarar miyagun ƙwayoyi da kuma yadda wasu ƙungiyoyin masu fataucinsu ke amfani da nahiyar Afirka a matsayin hanyar jigilar kayayyakin zuwa Turai.