An bayyana wannan buƙata ne a cikin sanarwar matsayin Najeriya kan ajandar 138 mai taken Shirin Kasafin Kuɗi na 2027: Tsarin Masu Kula da Ayyukan MDD, wadda shugaban ma'aikatan gwamnatin tarayya, Olumuyiwa Enitan Abel, ya gabatar a zaman cikakken taro na 10 na kwamitin kula da harkokin gudanarwa da kasafin kuɗi na Majalisar Ɗinkin Duniya, a ƙarƙashin babban taronta na 81 da aka gudanar a birnin New York na ƙasar Amurka.

Najeriya ta jaddada cewa ƙarfafa tsarin masu kula da ayyukan MDD wani muhimmin buri ne da ƙasashe mambobin ƙungiyar ke da alhakin cimmawa, domin bunƙasa haɗin gwiwar ƙasashen duniya da inganta ayyukan raya ƙasa na Majalisar.

Ta bayyana cewa samar da ingantaccen tsarin da ke da isassun kuɗaɗe zai taimaka wajen tabbatar da cewa tallafin raya ƙasa da MDD ke bayarwa ya dace da buƙatu da manufofin ƙasashen da ake tallafawa.

Najeriya ta kuma jaddada cewa samar da isassun kuɗaɗe masu ɗorewa da tabbas yana da matuƙar muhimmanci wajen kula da ayyukan haɗin gwiwa, riƙe ƙwararrun ma'aikata da kuma bai wa masu kula da ayyukan MDD damar gudanar da nauyin da ƙasashe mambobin ƙungiyar suka ɗora musu yadda ya kamata.

Ƙasar ta kuma bayyana muhimmancin wannan tsarin ga nahiyar Afirka, inda ta ce daga cikin ofisoshin masu kula da ayyukan MDD guda 132 da ke faɗin duniya, 53 suna nahiyar Afirka, wanda ya kai kusan kashi 40 cikin 100 na yawan ofisoshin da ke duniya.

Ta ce yawaitar ofisoshin a Afirka na nuna muhimmiyar rawar da suke takawa wajen taimaka wa ƙasashen nahiyar wajen aiwatar da manufofinsu na ci gaban ƙasa, ajandar MDD ta shekarar 2030 da kuma ajandar Tarayyar Afirka ta shekarar 2063.

Saboda haka, Najeriya ta yi kira ga ƙasashen da suka ci gaba na yankin Global North da su cika alkawuran da suka ɗauka na tallafa wa ƙasashe masu tasowa.

Ta kuma buƙaci manyan ƙasashen da ke bayar da tallafi da su ci gaba da ƙara yawan gudummawar da suke bayarwa ga tsarin raya ƙasa na Majalisar Ɗinkin Duniya, ta hanyar samar da kuɗaɗe masu ɗorewa, tabbatattu kuma na tsawon shekaru.