Ministan Tsaron Nijeriya, Christopher Musa, ne ya bayyana hakan a ranar Litinin, inda ya ce yarjejeniyar na cikin ƙoƙarin ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin ƙasashen domin yaƙi da ta’addanci, ayyukan ’yanbindiga da manyan laifuffukan da ake aikatawa a yankunan da ke tsakanin iyakokinsu.

A cewar Musa, yarjejeniyar za ta bai wa jami’an tsaro damar bin sawun mayaƙa da ’yanbindiga waɗanda ke ƙoƙarin tsere wa farmakin sojoji ta hanyar tsallakawa zuwa ƙasashe makwabta.

Ministan ya kuma bayyana cewa Nijeriya na samun bayanan sirri na kai tsaye, hotunan tauraron ɗan Adam da kuma tallafin horo daga Amurka domin ƙarfafa ayyukanta na yaƙi da ta’addanci.

Ya ce a baya-bayan nan ma, dakarun Nijeriya sun kashe ’yan ta’adda da dama, ciki har da jagororin ’yanbindiga, yayin wani samame da suka kai cikin dare a yankunan Arewa maso Gabas da Arewa maso Yammacin ƙasar.

Ana sa ran yarjejeniyar za ta taimaka wajen inganta tsaro a yankin arewacin Jamhuriyar Kamaru, inda hare-haren ƙungiyoyin Boko Haram da ISWAP suka shafe shekaru suna addabar al’ummomin da ke zaune a yankunan da ke iyaka da Nijeriya.

Sai dai har yanzu ba a fitar da cikakken bayani kan yadda za a aiwatar da yarjejeniyar ba, ciki har da ƙa’idojin gudanar da ayyukan sojoji da matakan kare fararen hula a yankunan da abin ya shafa.