Ma’aikatar ta bayyana cewa an gano gawarwakin mutum 21, yayin da aka ceto mutum ɗaya bayan jirgin ruwan ya nutse a ranar 7 ga watan Nuwamba. Ta ce ana ci gaba da aikin ceto da neman sauran waɗanda suka ɓace.

Sai dai wasu kafafen yaɗa labarai sun bayar da rahoton cewa adadin waɗanda suka mutu ya haura haka.

Kamfanin Dillancin Labaran Senegal (SPA), mallakin gwamnatin ƙasar, ya ruwaito cewa an gano gawarwaki 35. Sai dai har yanzu BBC ba ta iya tabbatar da wannan adadi da kanta ba.

SPA ya kuma bayyana cewa jirgin ruwan na ƙoƙarin isa Tsibiran Canary na ƙasar Sifaniya ne, ta hanyar wucewa ta gabar tekun Mauritaniya.

Ana sa ran Ministan Harkokin Cikin Gida na Senegal, Mouhamadou Makhtar Cissé, zai kai ziyara wurin da hatsarin ya faru a ranar Litinin domin jajanta wa iyalan waɗanda suka rasu da sauran al'ummomin da lamarin ya shafa.

A nasa ɓangaren, shugaban ƙasar Senegal, Bassirou Diomaye Faye, ya riga ya miƙa saƙon ta'aziyyarsa ga iyalan waɗanda suka rasa rayukansu.