Wani bincike da cibiyar Pew Research Center ta gudanar ya nuna cewa, duk da cewa yawan mabiya Kiristanci na ci gaba da ƙaruwa, yawan Musulmai na ƙaruwa cikin sauri sakamakon yawan haihuwa a tsakanin al'ummar Musulmi.
Rahoton ya bayyana cewa ana ƙiyasin mace Musulma na haihuwar yara sama da uku a matsakaici, idan aka kwatanta da kusan yara biyu da rabi ga mace Kirista.
Ya ƙara da cewa tun shekaru shida da suka gabata, Musulmai sun kasance masu rinjaye a ƙasashe 53 na duniya.
Binciken ya kuma nuna cewa ana sa ran mafi yawan ƙaruwar yawan Musulmai za ta faru ne a ƙasashen da Musulmai suka fi yawa.
Haka kuma, cibiyar ta yi hasashen cewa yawan Musulmai a duniya zai ƙaru da ƙarin mutum biliyan 1.2 nan da shekarar 2070.
