Kamfanin ya bayyana cewa matsalar ta samo asali ne daga aikin inganta tsarin na’urorinsa, ba wai sakamakon wani harin kutse ta intanet ba.
A ƙasashe da dama, asibitoci, kotuna da kuma harkokin sufuri sun fuskanci matsaloli sakamakon katsewar ayyukan kamfanin. Sai dai Microsoft ya ce al’amura sun fara komawa daidai.
Rahotanni sun ce masu amfani da manhajojin kamfanin sun fara fuskantar matsaloli tun daga ranar Alhamis.
Ko da yake ba a bayyana ainihin adadin mutanen da abin ya shafa ba, kimanin mutum miliyan 430 ne ke amfani da manhajojin Microsoft, yayin da aka samu rahotannin matsalar daga ƙasashe sama da 70.
