Kamfanin ya ce yana gudanar da bincike domin gano musabbabin matsalar, tare da ɗaukar matakan da suka dace domin dawo da ayyukan manhajojin yadda ya kamata.

Microsoft ya kuma yi watsi da wasu rahotannin da ke nuna cewa matsalar na iya kasancewa sakamakon yunƙurin kai masa hari ta yanar gizo.

A cikin wata sanarwa da kamfanin ya fitar, mataimakin shugaban Microsoft, Charles Lamanna, ya bayyana cewa suna matuƙar baƙin cikin matsalar da ta kawo cikas ga masu amfani da ayyukansu, yana mai cewa kamfanin na ƙoƙarin shawo kanta.

Rahoton kamfanin Downdetector, wanda ke bibiyar matsalolin ayyukan intanet, ya nuna cewa katsewar ta shafi ƙasashe da yankuna 74 a cikin awa guda.

Daga cikin wuraren da abin ya shafa akwai New Zealand, inda rahotanni suka nuna cewa matsalar ta shafi ofisoshin jakadancin ƙasar da wakilanta a sassa daban-daban na duniya.

A Japan kuwa, Ministan Tattalin Arziki, Ryosei Akazawa, ya yi hasashen cewa matsalar za ta iya haifar da babban tasiri, saboda yawan mutanen da ke amfani da manhajojin Microsoft da abin ya shafa. Ya bayyana hakan ne a wata hira da jaridar Asahi Shimbun.

Da farko, Microsoft ya ce yana binciken rahotannin matsalar da aka samu a Amurka, amma daga baya ya tabbatar da cewa katsewar ta shafi haɗin kai da wasu ayyukan Microsoft 365 ga masu amfani, ba tare da la'akari da yankin da suke ba.

Kamfanin ya ce ma'aikatansa na ci gaba da ƙoƙarin dawo da ayyukan da abin ya shafa cikin gaggawa.