Ƙungiyar masu sayar da wayoyin hannu a jihar Kano ta bayyana damuwa kan matakin Hukumar Sadarwa ta Najeriya (NCC) na ƙarfafa aiwatar da tsarin tantance wayoyi da sauran na’urorin sadarwa da ke amfani da katin SIM a ƙasar.
Ƙungiyar ta ce tsarin na iya jefa ’yan kasuwar da ke sayar da wayoyin hannu, musamman tsofaffin wayoyi da aka fi sani da “London Used”, cikin matsaloli tare da janyo musu asarar kuɗaɗe da kuma barazanar rasa ayyukan yi ga matasa.
Ɗaya daga cikin mambobin ƙungiyar, Abubakar Ibrahim Ma’aji, ya ce wasu daga cikin wayoyin da suke sayarwa ba sa cikin nau’o’in da ake iya tantancewa ta tsarin hukumar.
Ma’aji ya bayyana cewa: “Ba dukkan nau’o’in wayoyin da muke sayarwa ba ne ake tantancewa. Wayoyin da ba sababbi ba, waɗanda ake kira London Used, suna cikin waɗanda muke sayarwa da yawa.”
Ya ƙara da cewa ’yan kasuwar sun riga sun kashe makudan kuɗaɗe wajen sayen wayoyin da suke hannunsu, don haka duk wani takunkumi da zai hana sayar da su na iya janyo musu babbar asara.
A cewarsa, wasu daga cikin wayoyin da suke sayarwa ana sayo su ne daga ƙasashen da ke makwabtaka da Najeriya, ba daga cikin ƙasar ba, saboda haka yana ganin ya kamata hukumar ta yi la’akari da yanayin kasuwancinsu wajen aiwatar da tsarin.
A nata ɓangaren, NCC ta bayyana cewa tsarin tantance na’urorin wani ɓangare ne na ƙarfafa aiwatar da dokokin da suka shafi amincewa da na’urorin sadarwa, domin tabbatar da cewa wayoyin da ake amfani da su a cibiyoyin sadarwar Najeriya sun cika ƙa’idojin fasaha da tsaro.
Hukumar ta ce tsarin na taimakawa wajen gano na’urorin da aka yi wa kwafin lambar IMEI, da waɗanda aka sace, da kuma na’urorin da ba su cika ƙa’idojin da aka gindaya ba.
A bayanin da NCC ta fitar, ta ce tsarin ya fara aiki ne tun ranar 7 ga Oktoba, 2026. Ta kuma bayyana cewa wayoyin da suka riga suka haɗu da cibiyoyin sadarwar Najeriya kafin wannan rana an tantance su ta atomatik.
Sai dai hukumar ta buƙaci masu shigo da wayoyi, dillalai da sauran masu sana’ar sayar da na’urorin sadarwa da su tabbatar da cewa kayayyakin da suke sayarwa sun cika ƙa’idojin amincewa da tantancewa.
NCC ta kuma samar da hanyar da masu sayar da wayoyi za su iya amfani da ita wajen tantance wayoyin da ke hannunsu, ciki har da waɗanda suka riga suka saya domin sayarwa.
