Hukumar ta bayyana cewa a baya-bayan nan ta kama wasu ’yan Afirka ta Kudu uku bisa zargin hannu a safarar miyagun ƙwayoyi, ciki har da hodar ibilis, heroin da tabar wiwi da aka sarrafa.

Mataimakin daraktan sashen watsa labarai da wayar da kan jama’a na NDLEA, Francis Okogun, ne ya bayyana hakan a Abuja ranar Alhamis, yayin wani taron manema labarai na haɗin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro da na tattara bayanan sirri.

Okogun ya yi zargin cewa wasu ’yan ƙasashen waje na amfani da Nijeriya wajen jigilar miyagun ƙwayoyi zuwa wasu ƙasashe ta haramtacciyar hanya, a madadin ƙungiyoyin fataucin miyagun ƙwayoyi na ƙasashen waje, yayin da wasu ke ƙoƙarin shigar da irin waɗannan ƙwayoyi cikin ƙasar.

Ya bayyana cewa kasancewar Nijeriya a Yammacin Afirka da kuma iyakokinta da ƙasashen Benin, Nijar, Chadi da Kamaru ya sanya ta zama muhimmiyar mahadar kasuwanci da zirga-zirga tsakanin Yammaci da Tsakiyar Afirka.

Ya ce hukumar na gudanar da bincike kan waɗannan kamen domin gano inda aka shirya kai miyagun ƙwayoyin da kuma ƙungiyoyin da ke da hannu a safarar su.

A cewarsa, an kama mutum uku a lokacin da ake nazari a kai, inda aka samu miyagun ƙwayoyi masu yawa a hannunsu, ciki har da heroin, hodar ibilis da kuma tabar wiwi da aka sarrafa, wadda aka fi sani da suna Loud.

Ɗaya daga cikin waɗanda aka kama ita ce Gebashe Sithandiwe Jessie, ’yar Afirka ta Kudu, wadda jami’an hukumar suka cafke a filin jiragen sama na ƙasa da ƙasa na Fatakwal a watan Oktoban 2026.

Ana zarginta da ƙoƙarin safarar tabar wiwi da aka sarrafa mai suna Thai Loud, mai nauyin kilogiram 32.74, wadda aka ɓoye a cikin kayayyakinta.

Haka kuma, an kama wata ’yar Afirka ta Kudu mai suna Will Jessica Ann, mai shekara 38, a filin jiragen sama na ƙasa da ƙasa na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja, a ranar 6 ga Yulin 2026, tare da bulo 14 na heroin masu nauyin kilogiram 5.75.

Okogun ya ce kamen na da muhimmanci saboda yawan miyagun ƙwayoyin da aka ƙwace da kuma alaƙar da ake zargin waɗanda aka kama ɗin suna da ita da ƙungiyoyin fataucin miyagun ƙwayoyi na ƙasa da ƙasa.

Ya ƙara da cewa NDLEA na ci gaba da gudanar da cikakken bincike domin gano sauran mutanen da ke da hannu a safarar miyagun ƙwayoyin da kuma ƙungiyoyin da ke jagorantar ayyukan.