Babban Sakataren Hukumar Yaƙi da Sauyin Yanayi ta Majalisar Ɗinkin Duniya, Simon Stiell, ne ya buɗe taron, inda ya yi kira ga mahalarta da su samar da ingantacciyar hanya ta haɗa kai wajen ɗaukar matakan da za su taimaka wajen yaƙi da matsalar sauyin yanayi.

A jawabinsa, Stiell ya jaddada cewa ya zama wajibi manyan ƙasashe su jagoranci ƙoƙarin samar da mafita ga matsalar, yana mai cewa akwai buƙatar aiwatar da yarjejeniyoyi da matakan da aka cimma a tarukan baya domin rage illolin sauyin yanayi da duniya ke fuskanta.

Taken taron na bana shi ne, “Daga tattaunawa da fahimtar juna zuwa aiwatarwa”, wanda ke nuna muhimmancin mayar da shawarwari da dabarun da ƙasashe suka amince da su zuwa ayyukan zahiri.

Daga cikin muhimman batutuwan da za a tattauna a taron akwai matakan yaƙi da sauyin yanayi, muradun ƙasashe wajen rage illolinsa, samar da kuɗaɗen tallafa wa ƙasashen da matsalar ta fi shafa, da kuma sauya amfani da makamashin da ke gurɓata muhalli zuwa makamashi mai tsafta.

Ana sa ran taron zai gudana na tsawon kwanaki 12, daga ranar 9 zuwa 20 ga watan Nuwamba, inda ake sa ran ƙasashe za su tattauna tare da samar da matsaya kan yadda za a hanzarta aiwatar da matakan yaƙi da sauyin yanayi.

A tsakanin ranakun 11 da 12 ga watan Nuwamba ne shugabannin ƙasashen da ke halartar taron za su gabatar da jawabansu, domin bayyana matsayinsu da shirye-shiryensu wajen tunkarar matsalar.

Sai dai ana gudanar da taron ne a daidai lokacin da ake fuskantar ƙalubalen rashin haɗin kai daga wasu manyan ƙasashe, ciki har da Amurka, wadda ta ɗauki matakin janye kanta daga wasu tsare-tsaren haɗin gwiwar yaƙi da sauyin yanayi.