Kotun Tarayya da ke Abuja ta soke dukkan matakan da suka kai ga zaɓen Atiku Abubakar a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC a babban zaɓen 2027.

Kotun ta kuma soke zaɓen tsohon Shugaban Majalisar Dattawan Nijeriya, David Mark, da Rauf Aregbesola da sauran mambobin jam’iyyar a matsayin shugabannin ADC na ƙasa.

A hukuncin da ya yanke ranar Alhamis, Mai Shari’a Peter Lifu ya ce an kuma soke zaɓen dukkan ’yan takarar da jam’iyyar ta gabatar domin shiga zaɓen 2027, saboda an ba su takardun takara ne ƙarƙashin shugabancin jam’iyyar da kotun ta bayyana a matsayin wanda bai dace da doka ba.

Mai shari’a Lifu ya amince da ƙarar da Nafiu Bala Gombe, tsohon Mataimakin Shugaban ADC na ƙasa, ya shigar, inda ya ƙalubalanci halaccin shugabancin jam’iyyar da David Mark ke jagoranta.

Gombe ya yi iƙirarin cewa bayan murabus ɗin tsohon shugaban jam’iyyar na ƙasa, Cif Ralph Nwosu, kundin tsarin mulkin ADC ya ba shi damar karɓar ragamar shugabancin jam’iyyar.

Saboda haka, ya nemi kotun ta soke dukkan matakan da shugabancin David Mark ya ɗauka, tare da hana Mark, Aregbesola, sakataren jam’iyyar na ƙasa da sauran mambobin kwamitin riƙon ƙwarya gabatar da kansu a matsayin halastattun shugabannin ADC.

Mai ƙarar ya kuma yi zargin cewa yadda aka naɗa shugabannin ya saɓa wa kundin tsarin mulkin ADC da kuma wasu tanade-tanaden dokar zaɓe.

Ƙarar mai lamba FHC/ABJ/CS/1819/2025 ta shafi jam’iyyar ADC, Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), David Mark, Rauf Aregbesola da Ralph Nwosu a matsayin waɗanda ake ƙara na farko zuwa na biyar.

A hukuncinsa, Mai Shari’a Lifu ya amince da buƙatun Gombe tare da ba shi dukkan abubuwan da ya nema a cikin ƙarar.

Sai dai hukuncin ba yana nufin an kawo ƙarshen burin Atiku Abubakar na neman kujerar shugaban ƙasa a 2027 ba, domin yana da damar ƙalubalantar hukuncin a Kotun Ɗaukaka Ƙara bisa tanade-tanaden dokokin da suka dace.

Da yake mayar da martani kan hukuncin, Sakataren Jin Daɗin Jama’a na ADC na ƙasa, Nkemakolam Ukandu, wanda aka shigar cikin ƙarar a matsayin mai ruwa da tsaki, ya ce jam’iyyar za ta ɗaukaka ƙara domin ƙalubalantar hukuncin.