A watan Janairun shekarar nan ne aka yi wa matar da ’ya’yanta shida kisan gilla da rana tsaka a cikin gidansu, lamarin da ya tayar da hankalin al’umma.

Kakakin kotunan jihar Kano, Baba Jibo Ibrahim, ya bayyana cewa an gurfanar da mutum uku a gaban kotun bisa zargin hannu a aikata kisan, sai dai kotun ta wanke ɗaya daga cikinsu bayan ta kasa samun hujjar da ke tabbatar da hannunsa a cikin laifin.

Ya ce kotun ta samu sauran mutanen biyu da laifi, inda ta yanke musu hukuncin ɗaurin rai-da-rai har sau shida bisa laifin fashi da makami.

Baya ga haka, kotun ta kuma yanke musu hukuncin kisa ta hanyar rataya har sau shida kowannensu bisa samunsu da laifin kashe matar da ’ya’yanta shida.

Baba Jibo Ibrahim ya ƙara da cewa waɗanda aka yanke wa hukuncin suna da wa'adin watanni uku domin ɗaukaka ƙara idan ba su gamsu da hukuncin kotun ba.