Umarnin kotun ya biyo bayan ƙorafin da wani mazaunin Ƙaramar Hukumar Gwarzo, Sulaiman Isah, ya shigar, inda ya zargi ɗan majalisar, wanda aka fi sani da Baban Gandu, da rushe masa gini, cin zarafinsa da kuma yi masa barazanar kisa kan wata takaddama da ta shafi sayen dukiya.

Mai ƙorafin ya yi zargin cewa rikicin ya samo asali ne daga sayen wata kadara da ya yi, wanda daga bisani ya haifar da saɓani tsakaninsa da ɗan majalisar.

Bayan sauraron ƙorafin, kotun ta umarci ’yan sanda da su gudanar da bincike domin gano gaskiyar zarge-zargen da kuma ɗaukar matakan da suka dace bisa tanadin doka.

Matakin kotun na nufin a binciki zarge-zargen da aka gabatar, amma ba ya tabbatar da cewa ɗan majalisar ya aikata laifukan da ake zarginsa da su ba.

Har yanzu, ba a bayyana sakamakon binciken ’yan sanda ko martanin Muazu Abdullahi-Gwarzo kan zarge-zargen ba.