Daraktan Binciken Manyan Laifuka na Kenya, Mohamed Amin, ne ya bayyana hakan yayin gabatar da ƙwayoyin da aka ƙwace ga manema labarai, inda ya bayyana nasarar samamen a matsayin wani babban ci gaba wajen yaƙi da safarar miyagun ƙwayoyi a ƙasar.
An gudanar da kamen ne a ƙarshen makon da ya gabata a gabar tekun Kenya, bayan jami'an tsaro sun samu bayanan sirri daga takwarorinsu na Tanzania, waɗanda suka kama wasu mutane bisa zargin safarar wasu nau'ikan ƙwayoyi.
Mahukuntan Kenya sun ce sun kama mutane uku a yayin samamen, ciki har da 'yan ƙasar Tanzania biyu da kuma wani ɗan ƙasar Uganda.
Wannan kamen ya zo ne shekara guda bayan wani samame makamancin haka da ya kai ga ƙwace kilogram 1,036 na Methamphetamine a Kenya, wanda aka bayyana a matsayin mafi girman irin wannan kamen da aka taɓa samu a tarihin ƙasar.
Haka kuma, tsakanin watan Janairu da Oktoban 2026, mahukuntan Kenya sun kama mutane 1,631 bisa laifukan da suka shafi safarar miyagun ƙwayoyi.
Kenya dai ta daɗe tana fuskantar ƙalubalen safarar miyagun ƙwayoyi sakamakon matsayinta a gabar tekun Indiya, lamarin da ya sa ƙasar ke ƙara ƙaimi wajen ƙarfafa matakan yaƙi da wannan fatauci.
