Ziyarar, wadda ta gudana daga ranar 14 zuwa 21 ga watan Nuwamba, wani ɓangare ne na haɗin gwiwa tsakanin hukumomin kwastam na Najeriya da Nijar, da nufin nazarin hanyoyin da takwarorinsu ke bi wajen yaƙi da barazanar tsaro daga ƙasashen waje.

Sa ido kan iyakoki, musayar bayanan sirri da haɗin gwiwa da sauran hukumomin tsaro na daga cikin muhimman batutuwan da aka mayar da hankali a kai yayin ziyarar.

Tawagar jami’an Najeriya, ƙarƙashin jagorancin Mataimakiyar Kontrola IG Etim, ta ƙunshi jami’ai 13 masu matsakaicin matsayi a Hukumar Kwastam ta Najeriya, waɗanda ke cikin ɗaliban da ke karatu a Makarantar Horas da Jami’an Kwastam da ke Gwagwalada, Abuja.

Kafar watsa labarai ta Actu Niger ta ruwaito cewa ziyarar wani ɓangare ne na shirin inganta ƙwarewar jami’an tare da ba su damar samun ƙarin horo domin ɗaukaka matsayinsu zuwa manyan jami’ai.

Tawagar ta samu tarba daga Mataimakin Daraktan Hukumar Kwastam ta Nijar, Kanal Mohamed Siddo Yacouba.

Ganawar ta bai wa ɓangarorin biyu damar tattauna muradun gwamnatocinsu da ƙalubalen da ke tattare da haɗin gwiwar hukumomin kwastam na ƙasashen biyu.

Daga nan ne jami’an Najeriya suka kai ziyara Ma’aikatar Kuɗi ta Nijar, inda Babban Sakataren Ma’aikatar ya tarbe su.

Ƙarfafa dangantakar ƙasashen biyu

Yayin ganawar, Babban Sakataren Ma’aikatar Kuɗin Nijar ya yi maraba da tawagar tare da yaba wa shirin ziyarar, yana mai ƙarfafa gwiwar ci gaba da inganta haɗin gwiwa tsakanin Najeriya da Nijar.

Ya jaddada muhimmancin karewa da ƙarfafa dangantakar ƙasashen biyu, musamman a fannin tsaron kan iyakoki.

Ya kuma bayyana cewa ci gaba da musayar bayanai da ƙarfafa dangantakar aiki a wannan fanni na da matuƙar muhimmanci wajen inganta haɗin gwiwar hukumomin tsaro da tabbatar da tsaron iyakokin ƙasashen biyu.

Bayan ganawar ne aka fara zaman ƙarin ilimi a ɗakin taro na Ma’aikatar Kuɗi, inda aka buɗe jerin tattaunawa kan dabarun da Hukumar Kwastam ta Nijar ke amfani da su wajen tinkarar barazanar tsaro daga ƙasashen waje.