Hukumar ta ce Meta ba ta sanar da kusan masu amfani da Facebook miliyan 20 yadda ya kamata ba cewa manhajar na iya samun damar shiga hotuna da bidiyon da ke cikin wayoyinsu.

Ta bayyana cewa hakan na faruwa ne ta hanyar wani fasali da ke bai wa Facebook damar amfani da hotunan da ke cikin wayar wajen ba da shawarwarin abubuwan da masu amfani za su iya wallafawa a shafukansu.

Hukumar ta kuma bai wa Meta wa'adin kwanaki 60 domin dakatar da amfani da wannan fasali a matsayin tsarin da ke kunne tun farko, tare da umartar kamfanin da ya riƙa neman izinin masu amfani kai tsaye kafin samun damar amfani da irin waɗannan bayanai.

Wannan tara na daga cikin manyan tarurrukan kuɗi da hukumomin Italiya suka taɓa kakabawa wani babban kamfanin fasaha.