A wata hira da ya yi da wani shirin talabijin a Iran, jami’in ya ce ba za a bai wa hukumar damar shiga cibiyoyin ba har sai an cika sharuɗɗan da ƙasarsa ta gindaya.

Gharibabadi ya ce duk da cewa Iran mamba ce a yarjejeniyar hana yaɗuwar makaman nukiliya ta duniya, wato NPT, hukumar IAEA ta yi abin da ya kira siyasantar da aikinta, ba tare da mutunta wajibcin da ke tsakanin ɓangarorin biyu ba.

Ya ƙara da cewa matuƙar ba a kawo ƙarshen yaƙin ba, kuma Amurka ba ta cika nauyin da ya rataya a wuyanta ba, Iran ba za ta amince wa masu binciken hukumar su shiga cibiyoyin nukiliyarta ba.

Ya zuwa yanzu, Tehran ba ta bai wa masu binciken IAEA damar komawa ko ɗaya daga cikin cibiyoyin nukiliyarta da hare-haren Amurka da Isra’ila suka lalata ba.

A sabon rahotonta, hukumar IAEA ta bayyana cewa hare-haren Amurka da Isra’ila sun haifar da wani yanayi da ba a taɓa fuskanta ba, sai dai ta buƙaci Iran da ta bai wa masu binciken Majalisar Ɗinkin Duniya damar komawa cibiyoyin nukiliyarta domin gudanar da bincike.