Hare-haren, waɗanda rundunar sojin sama ta haɗin gwiwa ta kai ƙarƙashin Operation HADIN KAI, sun gudana tsakanin 16 da 17 ga Nuwamban 2026, inda aka kai hari kan wasu wurare da ake zargin ƴan ta'addan ISWAP suna amfani da su a Monguno da kudancin Tafkin Chadi.
A cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar ranar Laraba, 18 ga Nuwamba, ta ce an gudanar da hare-haren ne bayan samun bayanan sirri da ke nuna cewa ƴan ta'addan ISWAP na shirin kutsawa yankin Monguno.
Binciken sa ido na rundunar ya gano wasu ƴan ta'adda ɗauke da makamai suna tafiya ta wata hanyar daji a arewa maso gabashin garin, lamarin da ya sa aka kai musu hari ta sama.
Rundunar ta ce an kashe ƴan ta'adda bakwai a harin, ciki har da wasu da ke aiki a cibiyar ƙera bama-bamai da ake dasawa a kan hanyoyi (IED) ta ƙungiyar.
A wani hari na daban da aka kai a Arinna, da ke kudancin Tafkin Chadi, sojojin Najeriya sun ce sun kashe wasu ƴan ta'addan ISWAP da dama, lamarin da suka bayyana a matsayin babban koma-baya ga tsarin shugabancin ƙungiyar.
Rundunar sojin ta ce Abba Bomma, wanda ake zargin ya ƙware wajen ƙera abubuwan fashewa a ƙungiyar ISWAP, ya samu mummunan rauni tare da wasu ƴan ta'adda huɗu.
Kazalika, wasu manyan ƴan ta'addan ISWAP, ciki har da Mallam Sharki da Abu Saad, na cikin waɗanda hare-haren saman suka kashe.
Rundunar ta ƙara da cewa an kashe wasu ƴan ta'adda 12 tare da jikkata wasu biyar sosai a harin, yayin da aka lalata babura da dama mallakin ƙungiyar.
A cewar rundunar, hare-haren biyu sun yi sanadin kashe ƴan ta'addan ISWAP 21 tare da jikkata wasu 10.
Ta ce hare-haren sun raunana tsarin shugabancin ƙungiyar, tare da tarwatsa cibiyarta ta ƙera bama-bamai da kuma rage ƙarfinta na kai hare-hare a yankin.
Kwamandan rundunar ayyukan soji a yankin ya ce za su ci gaba da matsin lamba kan ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai har sai an dawo da zaman lafiya da harkokin yau da kullum a arewa maso gabashin Najeriya.
Ya kuma buƙaci mazauna yankin da su ci gaba da bai wa jami'an tsaro sahihan bayanai cikin lokaci domin taimakawa ayyukan yaƙi da ta'addanci.
ISWAP, wadda ke da alaƙa da ƙungiyar ta'addanci ta Daesh, na ci gaba da zama babbar barazana ga tsaro a arewa maso gabashin Najeriya, musamman a jihar Borno da yankunan da ke kewaye da Tafkin Chadi.
