Gwamnatin ta mayar da martanin ne ta hannun mai taimaka wa shugaban ƙasar na musamman kan kafafen sada zumunta, Dada Olusegun, wanda a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X ya bayyana ƙididdigar a matsayin farfagandar ’yan adawa.
Mista Olusegun ya ce ba gaskiya ba ne cewa shugabannin Najeriya 16 da suka gabata sun karɓi bashin Naira tiriliyan 46 kacal cikin shekaru 63.
Ya bayyana cewa ƙididdigar da aka fitar a ƙarshen shekarar 2022 ba ta haɗa da bashin wucin gadi na Naira tiriliyan 22.7 da gwamnatin Najeriya ta karɓa daga Babban Bankin Ƙasar (CBN) ba.
Ya kuma ce an ƙididdige basukan baya ne bisa farashin musayar dala ɗaya kan Naira 448, wanda shi ne farashin gwamnati a lokacin, alhali kuwa a kasuwar bayan fage dala ta kai sama da Naira 700.
A cewarsa, dole ne a samu bambanci a yawan bashin idan aka ƙididdige shi da sabon farashin musayar kuɗi, musamman bayan gwamnatin Tinubu ta bar darajar Naira ta kasance bisa tsarin kasuwa tun watan Yunin 2023.
Sai dai ƙididdigar Ofishin Kula da Basukan Najeriya (DMO) ta nuna cewa zuwa watan Yunin 2023, jimillar bashin ƙasar ya kai Naira tiriliyan 87 da biliyan 380.
Ƙididdigar ta nuna cewa zuwa watan Yunin 2026, bashin ya haura Naira tiriliyan 166 da biliyan 790.
Wannan na nufin an samu ƙarin bashin da ya kai kusan Naira tiriliyan 79 da biliyan 410 cikin shekaru uku.
