Gwamnatin Tarayya ta musanta zargin cewa tana da hannu a hukuncin da Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yanke, wanda ya soke shugabancin jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ƙarƙashin jagorancin Sanata David Mark, tare da rushe matakan da suka samar da tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar a zaɓen 2027.

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Ƙasa, Alhaji Mohammed Idris, ya ce gwamnatin Najeriya ba ta da hannu a hukuncin kotun, yana mai cewa duk wanda bai gamsu da hukuncin ba ya kamata ya bi hanyoyin shari’a domin neman hakkinsa.

Wannan martani na gwamnati ya biyo bayan kalaman Atiku Abubakar, wanda ya soki hukuncin kotun tare da nuna damuwa kan lokacin da aka yanke shi.

A cikin sanarwar da Daraktan Yaɗa Labarai da Dabarun Sadarwa na Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Atiku, Phrank Shaibu, ya fitar, tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya bayyana hukuncin a matsayin wani yunƙuri na raunana jam’iyyar ADC da kawo cikas ga burinsa na neman shugabancin Najeriya.

Atiku ya kuma bayyana cewa zai ƙalubalanci hukuncin a Kotun Ɗaukaka Ƙara, yana mai cewa akwai wasu batutuwan shari’a da ya kamata a sake dubawa.

Kotun, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Peter Lifu, ta yanke hukuncin ne a ranar Alhamis, 5 ga Nuwamba, 2026, bayan sauraron ƙarar da Nafiu Bala Gombe, tsohon Mataimakin Shugaban ADC na Arewa maso Gabas, ya shigar kan halaccin tsarin da ya samar da shugabancin David Mark.

Hukuncin ya kuma shafi sauran matakan da shugabancin ya ɗauka, ciki har da zaɓen fidda gwani da ya samar da Atiku a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar.