Da yake jawabi a wani taro da aka gudanar a gidan gwamnatin Kano ranar Litinin, Gwamna Yusuf ya ce ya amince da rabuwar aurensu, kuma tuni aka bayar da takardar saki.

Ya ƙara da cewa ya umarci Kwamishinan Yaɗa Labarai na jihar da ya fitar da sanarwa a hukumance domin kawo ƙarshen ce-ce-ku-cen da ake yi kan batun.

Cikin raha, gwamnan ya shaida wa mahalarta taron cewa komawa daga mata biyu zuwa mace ɗaya tamkar rage masa matsayi ne, don haka ya ce zai ci gaba da auren mata fiye da ɗaya.

Ya kuma buƙaci al’ummar jihar da su taya shi da addu’ar samun matar da ta dace, mai kyakkyawar tarbiyya.

Wannan furuci na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan rahotanni sun bayyana cewa Zainab ta shigar da ƙara a wata kotun yanki da ke Gudu, Abuja, inda ta nemi a raba aurensu.

Batun rabuwar auren ya ja hankalin jama’a, musamman duba da rikicin siyasar da ya ɓarke tsakanin gwamnan da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso bayan sauya sheƙar Gwamna Yusuf zuwa jam’iyyar APC.