Hukumar ta ce haɗurran da suka auku a wannan lokaci sun kai kimanin 7,000, inda kuma mutane 22,292 suka samu raunuka.

Shugaban hukumar ta FRSC, Shehu Mohammed, ne ya bayyana waɗannan alkaluma yayin gabatar da bayanan haɗurran a birnin Abuja.

Haɗurran ababen hawa na ci gaba da zama babban ƙalubale a Najeriya, inda ake danganta su da abubuwa da dama da suka haɗa da rashin kyawun hanyoyi, tuƙin ganganci, wuce gona da iri wajen gudu, da kuma rashin bin dokokin hanya.

A nasa jawabin, Kakakin hukumar FRSC a jihar Jigawa, Yahaya Ibrahim Yahaya, ya yi ƙarin bayani kan manyan dalilan da ke haddasa haɗurran ababen hawa, tare da jaddada muhimmancin kiyaye dokokin hanya domin rage asarar rayuka.