FIFA ta sanar da kafa kwamitin ne watanni uku bayan shugabannin NFF sun ajiye muƙamansu.
Hukumar ta naɗa lauya Sampson Ebomhe a matsayin shugaban kwamitin, wanda ya ƙunshi fitaccen ɗan jarida, Godwin Enakhena, da masana harkokin gudanarwa biyu, Ms Amina Yerima da Dr Joe Abah.
Tsohon kyaftin ɗin tawagar Super Eagles, Daniel Amokachi, shi ne mutum na biyar a cikin kwamitin.
A cikin wata sanarwa da Babban Jami'in FIFA mai kula da ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa mambobi ya fitar, hukumar ta ce sabbin mambobin kwamitin za su fara aiki nan take, amma za su bi tantancewar cancanta ƙarƙashin tsarin FIFA na duba cancantar waɗanda aka naɗa.
Sanarwar ta ƙara da cewa tabbatar da mambobin zai dogara ne kan sakamakon binciken cancantarsu.
Haka kuma, FIFA ta bayyana cewa babu wani daga cikin mambobin kwamitin da zai samu damar tsayawa takara a zaɓukan NFF da za a gudanar nan gaba.
FIFA ta bai wa kwamitin wa'adin gudanar da aikinsa har zuwa ranar 31 ga Mayun 2027, tare da tsara masa wasu ayyuka na musamman baya ga kula da harkokin yau da kullum na NFF.
Daga cikin ayyukan da aka ɗora wa kwamitin akwai sake duba dokokin NFF domin faɗaɗa wakilcin masu ruwa da tsaki, tabbatar da daidaiton wakilci a kwamitin zartarwa na hukumar, da kuma rage yawan mambobin kwamitin.
Ana sa ran matakan za su taimaka wajen inganta tsarin gudanarwa da tabbatar da ingantaccen shugabanci a ƙwallon ƙafar Najeriya.
